Syria: Kungiyar Yan Ta’adda Ta “Kasd” Ta Yi Garkuwa Da Mutanen Dairzur Da Dama

 

Kungiyar ‘yan ta’adda daga kabilar Kurdawan kasar Siriya, wacce take samun goyon bayan Amurka ta yi garkuwa da mutanen garin Dairzur a gabacin kasar ta Siriya.


Majiyar muryar Jumhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa Kurdawan ‘yan kungiyar “Dakarun Democradiyyar Siriya” ko (QASD) sun yi garkuwa da mutanen ne a jiya Talata, don hana su zanga-zangar neman ficewar mayakan na su da kuma na sojojiin Amurka ‘yan ta’adda daga yankin.


Tun shekara ta 2011 ne gwamnatin kasar Amurka ta shigo da sojojinta cikin kasar Siriya da sunan yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh, wacce ta kirkokin. Sannan it ace ta samar da kungiyar KASD ta kurdawa wadanda ta kodaitar da su ballewa daga kasar ta Siriya.


Sannan a halin yanzu bayan nasarorin da gwamnatin kasar Siriya da kawayenta suka samu kan ‘yan tadda a mafi yawan lardun kasar, Amurka tana hada kai da kungiyar kundawan don satar arzikin yankin Arewa maso gabacin kasar Siriya daga cikin har da danyen man fetur.

SOURCE: ABNA24.COM


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com 

Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post