Chang Song-min, tsohon mai taimakawa tsohon shugaban kasar Koriya ta Kudu, Kim Dae-Jung, ya tabbatar da cewa kasar Koriya ta Arewa na boye gaskiyar halin da shugabanta ke ciki, duk kuwa da rahoton da aka bayar na cewa an dauki hoton Kim a 'yan kwanakin nan.
Wasu hotuna dake ta yawo a ranar Alhamis 20 ga watan Agusta, sun nuna yadda Kim ya halarci wani taro na gwamnati, sai dai kuma manyan kafofin yada labarai sunce baza su iya tabbatar da gaskiyar wadannan hotuna ba.
Da yake hira da manema labarai, Chang Song-Min ya ce: "Ina da tabbacin yana kwance babu lafiya, amma rayuwar shi bata kare ba har yanzu." Ya bayyana cewa tuni kasar ta Koriya ta Arewa ta mika wasu tsari na mulkin kasar ga kanwar shugaban kasar Kim Yo-Jong mai shekaru 33.
Chang ya kara da cewa: "Har yanzu dai ba a mika komai a hannunta ba, saboda haka an fara shigo da Kim Yo-Jong cikin tsarin mulkin ne saboda ba a da tabbacin abinda zai faru nan gaba."
Wannan dai ya zo ne bayan hukumar leken asiri ta kasar Koriya ta Kudu ta ruwaito cewa Kim zai mika ragamar mulkin kasar ga kanwarshi Kim Yo-Jong, domin ya saukakewa kanshi duk kuwa da karancin shekarunsa.
Hukumar ta kara da cewa shugaban kasar zai cigaba da juya ragamar mulkin kasar ta bayan daki, inda ta bayyana cewa hakan bashi da nasaba da rashin lafiyarsa. A watan Afrilu dai an samu jita-jita cewa shugaban kasar ya mutu, amma sai daga baya aka gano gaskiya bayan an nuno shugaban kasar a wajen bude wani kamfanin takin zamani.
SOURCE: LEGIT.NG
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com