Shugaban Kasar Lebanon Ya Sha Alwashin Fallasa Gaskiyar Yadda Aka Sami Fashewa A Tashar Jiragen Ruwa Na Beirut

Shugaban kasar Lebanon Michel Aun ya bayyana cewa sai ya fallasa wadanda suke da hannu a fashewar tashar jiragen ruwa na Beirut.

Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka ne a shafinsa na twitter a jiya Talata, ya kuma kara da cewa , tuni an mikawa ma’aikatar shari’ar kasar takardun binciken da aka gudanar dangane da fashewar a yau.

Har’ila yau ma’aikatar shari’a ta kasar ta Lebanon ta bada sanarwan cewa, ta bada sammashin kama mutane 20 wadanda ake tuhuma da hannu cikin fashewar.

A ranar 4 ga watan Augustan da muke ciki ne wasu abubuwa suka fashe a dakunan ajiyar kayayyaki a tashar jiragen ruwa ta Beriut babban birnin kasar ta Lebanon. Fashewar dai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 171, sannan wasu kima dubu 6 suka ji rauni.

Banda haka dubbai kuma suka rasa gidajensu. Har’ila yau an yi asarar kadarori wadanda aka kiyasta kimarsu da dalar Amurka billiyon 15.

SOURCE: ABNA24.COM


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com 





Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post