* MA'ASUMIYAH NIGERIAN NEWS UPDATES *
Tabbas, abinda aka kawo ne cikin littattafai cewa Yazid (L.A) ba shi ya kashe Imam Hussaini ba, kuma ma bai yi farin ciki da hakan ba.
Amsar wannan tambaya ba za ta samu ba har sai an biyo mu cikin wannan gajeren rubutu namu.
A lokacin da aka shigar da iyalan Ma'aiki (S) cikin fadar Yazid, sai Sayyida Fatima da Sakina (S.A) suka ga kan Imam Hussaini da Yazid ke boye shi gare su sai suka fashe da kuka.
Ganin kukan da Iyalan Annabi (S) ke yi yasa matan Yazid da 'ya'yan Mu'awiyya suka fashe da kuka.
Sai Sayyida Fatima (S.A) ta cewa Yazid (L A);
" Yanzu halin da 'ya'yan Manzon Allah (S) suka shiga ya faranta ma rai yaa Yazid "?
Sai yace;
" WALLAHI BAI FARANTA MIN RAI BA, KUMA NI ME QYAMATAR WANNAN (ta'addanci) NE ."
A lokacin ne Sayyida Sakina take cewa; " BAN TABA GANIN WANDA YA KAFIRCEWA ALLAH KAMAR YAZID BA ."
Daga nan Yazid ya umarta da a shigo mar da Imam Zainul-Abideen (A.S) a tantanke. Sai Aliyu yace;
" Yaa Yazid, da ace Manzon Allah (S) zai ganmu a tantanke da zai since shi daga gare mu ."
Sai Yazid yace;
" KA YI GASKIYA ."
Sai yayi umarni da a since shi. Sai yace;
" Da ace Manzon Allah (S) zai ganmu a gefe da zai so ya kusance mu ."
Sai yayi umarni da a matso da shi. Yazid yace;
'' YAA ALIYU, BABANKA NE YA YANKE ZUMINCINA, YA JAHILCI HAQQINA, KUMA YA FICE DAGA IKONA, SHI YASA KAGA ABINDA YA FARU DA SHI ."
Sai Imam Zainul-Abideen (A.S) yace;
" Babu abinda ke fatuwa na musiba cikin qasa ko a kanku face yana nan (rubuce) cikin littafi tun gabanin ya auku, kuma hakan me sauqi ne gun Allah. Don kada kuyi baqin ciki akan abinda ya kubuce muku, (Ku kuma) kada kuyi farin ciki da abinda aka ba ku, lalle Allah ba ya son dukkan mai taqama mai fahari ."
(Hadid:22-23).
Sai Yazid (L.A) yace;
" KUMA ABINDA YA SAME KU DAGA MUSIBA SAKAMAKON ABINDA HANNAYENKU NE SUKA AIKATA ."
(Shurah:30)
Daga wakilanmu na Bauchi Zone.
Tare da Ado Isah Guda
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com