Jagoran Harkar Musulunci, Samahatu Sayyid Ibrahim Yaqub Al-Zakzaky (H) ya sake aikawa da wani tallafin na magunguna da gidan sauro (Mosquito nets) ga sansanin 'yan gudun hijira da ke karamar hukumar Faskari ta Jahar Katsina.
Wanda wakilin 'yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky (H) na garin Funtua, Malam Rabi'u Abdullahi tare da sauran 'yan uwa suka kai tallafin amadadin Jagora (H).
Tallafin Shehin Malamin ya kunshi Magunguna daban daban kamar su: Magungunan Zazzabin cizon sauro (Anti-Malaria), Zazzabin typhoid (Antibiotics for Typhoid fever), Lamoniya (Pneumonia), Magungunan Zawo
(Anti-diarrheals), Magungunan macijin ciki na yara da manya (Anti-worms), gyambon ciki (Ulcer drugs), Magungunan karin jini (Blood tonics), Magungunan rage zugi (Pain relievers), Maganin zawon kananan yara (Zinc) da sauran su, tare
da gidan sauro (Mosquito nets).
Sakon Shehin Malamin ya isa hannun raunanan bayin Allah din dake sansanin gudun hijiran a yau Talata 18-Augusta-2020.
Su dai wadan nan 'yan gudun hijira mutane ne daga garuruwa daban daban, akwai mata, tsofaffi da yara kanana da aka baro da su daga mahaifar su da karfin tsiya, sakamakon tarwatsa su da mahara sukai.
Wanda a yanzu haka duk an koresu garuruwan su, duk abunda suka mallaka an raba su da shi.
Basu da komai, ba kuma su da muhallin da zasu zauna a halin yanzu.
Irin wannan tsananin rayuwa da azzaluman mahukuntan kasar nan suka sa wadan nan bayin Allah aciki yasa a ranar 9-7-2020 'yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky (H) na garin Funtua suka je suka ziyarce su tare da basu tallafin kayan abinci, Omo, sabulan wanka da wanki.
Sannan kuma a ranar Juma'a 31-7-2020 Jagoran Harka Islamiyya wanda ya tarbiyyantar damu tausayawa ga raunana da kan shi ya aika da tallafin kayan abinci ga wannan sansanin 'yan gudun hijira, domin tausayawa ga wannan mummunan halin rayuwa da gwamnatin kamakarya ta General Buhari (L) tasa su aciki.
Wadan nan bayin Allah sun nuna jin dadin su da wannan tausayawa da kulawa da Jagoran Harka Islamiyya Shaikh Zakzaky (H) yake nuna musu. Haka suma ma'aikatan wajen sun nuna farin cikin su sosai ga wannan sako na Shaikh Zakzaky (H).
Muna fatan Allah (SWT) Ya tausaya mana ba don halinmu ba Ya gaggauta kubutar da macecin wannan al'umma daga hannun macutan wannan al'umma
Ga Hotunan Da Muka Dauko Maku👇👇
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com