​Sayyid Nasrullah: Kulla Alaka Tsakanin UAE Da Isra’ila Cin Amana Ne Ga Musulunci

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana kulla alaka tsakanin hadaddiyar daular larabawa da Isra’ila da cewa, aiki ne na cin amana ga addinin muslunci da al’ummar Falastinu da ma larabawa baki daya.

A daren jiya ne Sayyid Hassan Nasrullah ya gabatar da wani jawabi a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon, dangane da cikar shekaru 14 da gwabza yaki tsakanin Hizbullah da Isra’ila, wanda Isra’ila ta janye da kanta sakamakon asarorin da ta tafka a yakin, wanda ba ta taba yin asara irinta ba a tarihi, ta fuskar yawan sojojinta da mayakan Hizbullah ta halaka, da kuma asarori na kayan yaki, da kuma yawan makamai masu linzami da Hizbullah ta antaya a cikin biranen Falastinu da yahudawa suka mamaye.

A cikin jawabin nasa Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, dukkanin nasarorin da kungiyar ta Hizbullah ta samu a yakin, sakamako na dogaro da Allah da kuma juriya da sanin manufa da sadaukarwa, gami da goyon baya da kwarin gwiwa da ta samu daga al’ummar kasar Lebanon.

Dangane da kulla alaka tsakanin hadaddiyar daular larabawa da Isra’ila da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata kuwa, Nasrullah ya bayyana cewa, wannan cin amana ne ga dukkanin al’ummar musulmi da wurare masu tsarki na addinin muslunci, da kuma al’umar falastinu da ma dukkanin larabawa.

Ya ce wannan ba sabon lamari ba ne, domin kuwa kasashe UAE da Saudiyya sun jima suna da alaka ta boye tsakaninsu da gwamnatin yahudawan Isra’ila, yanzu ne dai lamarin ya fara bayyana a fili, kuma za a ci gaba da ganin haka anan gaba.

Ya kara da cewa babbar manufar hakan ita ce samar wa Trump wani makami da zai iya yin amfani da shi a siyasarsa ta waje wajen lashe zaben shugaban kasa, da kuma kokarin tsamo Benjamin Netanyahu daga matsalar da ya shiga, inda a kullum yake fuskantar zanga-zanga daga yahudawa, bisa zarginsa da gazawa a dukkanin bangarori a siyasarsa.

Nasrullah ya ce abin takaici shi ne, abin da ya dami wadannan sarakunan larabawa shi ne neman yardar Amurka, domin ta ba su kariya su dawwama a kan mulki, domin hatta gabar da suke yi da Iran suna taya Amurka, ba wai domin suna da wata matsala da Iran ba, ko kuma da gaske suna ganinta a matsayin barazana gare su ba, amma domin su burge Amurka suna nuna wa Iran tsanin gaba da kiyayya.

SOURCE: ABNA24.COM

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post