Sayyid Hassan Nasrallah: Anan Gaba Zan Yi Tsokaci Akan Abinda Ya Faru Akan Iyaka Da Palasdinu Da Ke Karkashin Mamaya

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sayyid Hassan Nasrallah wanda ya gabatar da jawabi na dararen Muharram a jiya Laraba, ya ce; Abinda ya faru a kudancin Lebanon yana da matukar muhimmanci a gare mu, kuma nan gaba zan yi tsokaci a kansa.

ABNA24 : Sayyid Nasrallah ya jinjinawa ‘yan gwagwarmaya da su ka jikkata da kuma iyalansu, wadanda a kodayaushe su ke cikin fagen daga.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma kara da cewa; Tare da matsanancin halin da ake ciki, ‘yan gwagwarmayar ba su yin kasa a giwa wajen amsa kira da sadaukar da kai.

Sayyid Nasrallah dai yana yin tsokaci ne akan harin da sojojin HKI su ka kai a kudancin Lebanon da makamai masu dauke da sanadarin Phosphorus a daren Laraba.

SOURCE: ABNA24.COM

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post