Hukumar tsaro ta farin kaya da aka fi sani da DSS sun rubuta wata takardar sirri, inda suka aikawa shugabannin tsaron Jihohin Nijeriya musamman ma na Arewacin kasarnan, akan cewa wadanda suka kira da 'IMN' na shirye-shiryen tada "rikici da yamutsi" a birnin tarayya Abuja da kuma ma wadansu jihohin kasarnan. Inda a cewar rahoton da suka rubuta, tuni ma aka horas da matasan da za su yi wannan aikin wadanda aka tattaro su daga wadansu jihohin Nijeriya ciki kuwa harda Kudancin kasarnan.
Hukumar tsaron ta tabbatar da cewa wadannan "matasan" da suka kira da cewa; "ana tattaro su da horas da su," wani ne da suka kira da "Ammar Muhammad Rajab" shi ne wanda yake tara kudin da zai rabawa matasan domin su shigo birnin tarayya Abuja "su tada hargitsi da yamutsi."
A don haka sun nemi da a cafko shi wannan "Ammar Muhammad Rajab" din domin dakile shirin wadanda suka kira da "IMN."
A takaice halin da ake ciki ke nan..... Karin bayani da karin haske yana nan tafe daga baya.
-Ammar M. Rajab
04082020
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Labaran Duniya