​Rauhani: Bude Alaka Tare Da Isra’ila Shi Ne Kure Mafi Girma Da UAE Ta Tafka A Siyasarta

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana bude hulda ta diflomasiyya tsakanin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Isra’ila da cewa shi ne kure mafi girma da UAE ta tafka a tarihin siyasarta.


A lokacin da yake gabatar da wani jawabi a birnin Tehran, Rauhani ya bayyana cewa, idan UAE tana zaton cewa ta wannan hanya ne za ta karfafa tsaronta da kuma tattalin arzikinta, to kuwa ta tafka babban kure, domin hakan babu abin da zai jawo mata sai karin matsaloli.


Baya ga haka kuma, Rauhani ya ce abin da UAE ta yi babban cin amana ne ga al’ummar Falastinu, da ma dukkanin al’ummomin larabawa da na musulmi, kuma hakan yana matsayin tozarta masallacin quds da ke karkashin mamayar Isra’ila.


Shugaba Rauhani ya bayyana kulla alaka tsakanin UAE da Isra’ila da kuma hankoron da wasu daga cikin sarakunan larabawa na yankin suke yi na ganain su ma sun yi hakan, ba komai ba ne illa shirin Amurka, na neman ganin Trump ya samu nasara a zabe mai zuwa a kasar Amurka.


A daya bangaren kuma Rauhani ya gargadi UAE da cewa, idan ta kuskura ta bude wa Isra’ila hanya ta shigo cikin yankin tekun Fasha, to kuwa lamurra za su canja tsakanin Iran da UAE, domin kuwa Iran din za ta dauki matakin da ba zai yi wa UAE dadi ba.


SOURCE: ABNA24.COM


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com 


Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post