Rasha Da Sin Sun Rage Ciniki A Tsakaninsu Da Dalar Amurka Har Na Fiye Da Kashi 50%

Kasashen Rasha ta Sin sun rage ciniki da dalar Amurka a tsakaninsu har na kashi kasa da 50% a cikin watanni ukku na farkon wannan shekara ta 2020.

Kamfanin dillancin laraban Rasha Today ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergay Lavrov ya na cewa kasar Rasha ta fara siyasar kaucewa amfani da dalar Amurka a cinika tsakanint da Sin a duk inda hakan zai yu.

Kididdiga sun nuna cewa zuwa shekara ta 2016 yawan cinikayya tsakanin kasashen biyu tare da amfani da dalar Amurka ya kai kashi 90%. Amma a farkon wannan shekara zuwa yanzu sun rage yawan amfani da dolar Amurka har zuwa kashi 54%.

A halin yanzu dai cinikayya tsakanin kasashen biyu sun fi amfani da kudaden kasashen biyu, wato (Yen da Rubul) da kuma kudaden Yuro.

Tun lokacinda shugaban kasar Amurka mai ci Donal Trump ya shiga fadar White House ya dauki siyasar takurawa kasashen Rasha da Sin a fagage da dama, wadanda suka hada da tattalin arziki da tsaro.

SOURCE: ABNA24.COM

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post