Nijar Na Bikin Cika Shekaru 60 Da Samun ‘Yancin Kai



Yau Litini 3 ga watan Agusta 2020, Jamhuriyar Nijar, ta cika shekara 60 cif, da samun ‘yancin kai daga turawa ‘yan mulkin mallaka na Faransa.

Nijar dai ta samun ‘yancin kai ne a ranar irinta yau 3 ga watan Agusta na 1960.

Bikin na bana dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da manyan zabukanta a watan Disamba mai zuwa.

A cikin jawabinsa, na jajibirin ranar, shugaban kasar ta Nijar, Alhaji Isufu Mahammadu, wanda ya kore duk wata yiwuwar sake tsayawa takara, ya yi kira ga dukkan ‘yan siyasar kasar dasu bada goyan baya domin gudanar da zabukan kasar dake tafe cikin lumana da kwanciyar hankali.

Ana amfani da bikin wannan rana ta 3 uku ga watan Agusta, domin shuka itatuwa a wani mataki na yaki da gurgusowar Hamada, wanda a bana ake gudanar da shi a hukumance a jihar Agadas dake arewacin kasar karkashin jagorancin shugaba Isufu.

SOURCE: ABNA24.COM

DUBA SABBIN LABARAI ANAN: http://www.maasumah.com.ng

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN: @EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post