Yusuf arande
Cibiyar bincike a kan Farin ciki, ta bayyanar da wasu hanyoyi da mutane zasu iya bi don samun farinciki da annashuwa a rayuwar su. A binciken da aka gudanar, an dauki mutane dubu daya da casa’in da biyar 1,095 a kasar Denmark, an kuma raba yawan su gida biyu.
Kashi yada an basu damar amfani da shafin zumunta na facebook, daya rabin kuwa basa amfani da shafin, daya daga cikin masu gudanar da binciken ya bayyanar da abun da wasu ke cewa, suna amfani da shafin zumunta na facebook ne bisa dalilin, shine kawai wata hanya da matasa da tsofafi ke haduwa don tattauna wasu abubuwa a rayuwa.
Da dai aka bayyanar da sakamakon, kashi tamanin da takwas 88% na mutanene da basu yi amfani da shafin ba na tsawon sati daya, sun bayyanar da cewar gaskiya rashin amfani da shafin ya samusu farinciki fiye da lokacin da suke amfani da shafin. Su kuma wadanda basu yi amfani da shiba, kashi saba’in da biyar 75%. Hakan dai ya bayyanar da cewar duk lokacin da mutun yake shige-shigen irin wadannan shafufukan yanar gizon, yakan kara samun damuwa, musamman ma idan yaga wasu abubuwa da suka bata mishi rai, hakama yana iya ganin wadanda zasu faranta mishi rai. Don haka mutane su kokarta yin amfani da wadannan shafufukan ta yadda zai amfanar dasu da kuma cigaban kansu da al'umar su.
Tags:
Yanar gizo