"Nawa Ake Badawa Hakkin Shuhada A wata?" – Sayyid Zakzaky (H) Ya Tambaya.




Aka ce masa naira dari-dari ne.

Sai yace: "kaga ko da haka din ne ana ganinsa kadan, idan da mutum miliyan daya za su ba da naira dari-dari miliyan nawa kenan?" 

Aka ce Miliyan Dari.

Yace; "a wata kenan? To Amma (Mu'assasar Shuhada) Kun taba samun miliyan 100 kuwa (a shekara)?" 

Aka ce A'a. 

Shaikh (H) ya sake tambayar cewa; "Amma yan uwa sun haura miliyan daya ai ko?" 

Sai ya ce: "Naira dari daya a wata, kowa ne ya ba da. Kaga a wata za a samu miliyan 100, a shekara za a samu miliyan dubu da dari biyu kenan kenan. Kai! 1.2bn kenan."

Yace: "Amma ba a bayarwar ne, kowa sai ya zauna ya yi ta.... Kai Dan Adam da son abin Duniya yake. Kaga tabbatan ba a mikawa din ne, da ana mikawa, 'yan kadan kadan din kudin nan sai kaga sun tattaru. Kuma mutum ba zai ji a jikinsa ba. Yanzu jikinka zai fada maka don ka ba da naira dari a wata?" Ya tambayi yan uwa.

— A wajen wani Mu'utamar din Wakilan Mu'assasatu Shuhada'u a Zariya.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post