.
A tarihin mulki na duniya, tun daga kan na farko zuwa na yanzu, akanyi qoqarin fito da nasarorin mutum bayan gama mulkinsa. Ba a cika ambaton nasarorin ba aqallah sai bayan cika shekara, idan kuwa rubutawa ne a kundin tarihi to yawanci sai bayan gama mulki ake yi.
Amma shi wannan shugaba wanda nasarorinsa suka fi saurin bayyana yasa za mu ambaci kadan daga cikinsu kamar haka:-
.
(1)- Yayi nasarar damqe malaman 'Dariqa guda ( 123 ), tare da garqame su sama da kwana sittin ( 60 ), cikinsu kuwa har da mahaddata Qur'ani ( 80 ).
.
(2)-Yayi nasarar halakar da wadanda ake laqaba musu cewa masu munanan aqidu 'yan Shi'ah ( 23 ), tare da raunata wasu da dama daga cikinsu a hanyar su ta TATTAKI zuwa Zaria daga Kano, ta hanyar amfani da yaransa 'yan Boko Haram.
.
(3)- Tashin farashin kayan masarufi a kasuwanni, har abinda ake ganinsa a matsayin ( common ), wato ( pure water ).
.
(4)- Fito da sabon salon barnata arziqin qasa cikin hikima, ta hanyar qirqiro yawon gantali BA qaqqautawa.
.
(5)- Zama ministan man Fetur, Wanda hakan yayi sanadin tashin farashin ( litre ) zuwa #160-180 a gidajen mai.
.
(6)- Faduwar qimar ( darajar ) naira a kasuwar duniya.
.
(7)- Tunzura mata musulmi da maza masu kishin muslimci, ta hanyar barazanar haramta sanya Hijabi ga mata musulmi.
.
(8)- A matsayinsa na Shugaban Ahlus-Sunnah ( ga masu yimar kallon haka ), ya halasta musu abinda Allah ya haramta, wato yin hannu da matar da ba muharrama ba, ( ba tare da ya sami suka daga gare su ba ).
.
(9)- Sheqar da jinanan musilmi sama da dubu ( 1000 ) cikin awowi 48, qona gawarwaki, garqame masu munanan raunuka BA tare da barin anyi musu jinya ba. Tare da hakan kuma ya sami jinjina ta musamman daga malaman Qungiyoyin Izala.
.
(10)- Samun hadin kan Turai cikin qanqanin lokaci na amincewar taimaka masa wajen wargaje Qasar da yake mulka ( ganin cewa Shi ba 'Dan Qasar bane a sassala.
.
.
======== TAMBIHI ========
_____________________________________________
A tarihin kafuwar wannan qasa Nigeria, tun daga kan mulkin Soja har kan mulkin Farar Hula wacce tayi mulki na tsahon shekaru 16 ba a sami Shugaba da ya iya Samun wadannan nasarori a tsahon mulkin sai ba, amma wannan Shugaba ya cimma su cikin watanni tara (9).
.
======== TAMBAYA ========
_____________________________________________
(i)- Shin, me ya hana wadanda suka gabace shi cimma wadannan nasarori cikin tsahon mulkin su?
.
(ii)- Duk da cewa ya taba yin mulki a Soja wanda tsahon zamansa kan kujera yafi wannan, tare da cewa a wancan lokaci yafi samun qarfin iko wanda duk abinda yayi ba za a tuhume ba tunda ba mulkin Dimokaradiya ake yi ba, amma ya kasa cimma irin wadannan nadarori?
.
(iii)- Shin meye sirrin cimma wadannan nasarori cikin qanqanin lokaci da wasunsa suka gagara?
.
Lalle akwai buqatar jin wannan sirrin nasara don a rubuta su cikin Kundin tarihi don amfanuwa ga masu zuwa nan gaba ( future generation ).
.
======== QALU-BALE GA 'YAN ADAWA ========
____________________________________________
Kasantuwar duk nasarar da mutum ya samu cikin mulkinsa sai a sami 'yan adawa ga wadannan nasarori.
Qalu-balen da nake yiwa 'yan adawa anan shine, duk Wanda ke jayayya ko ganin wadannan nasarori ba su kai abinda za a ambata a matsayin nasarorinsa ba.
Ko kuma yana mana fassara da cewa an saye mu ne da kudade yasa muka fito muke tallarsa, ya fito nan ya nuna mana shugaban da ya taba cimma irin wadannan nasarori Cikin tsahon mulkin sa.
.
Idan kuwa mutum yasan bai tanadi hujjoji gamsassu ba, kada ya fito don sukar wadannan nasarori ( achievements ).
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com