✍️Auwal M Tukur
18/8/2020
Yan'uwana matasa barkan mu da sake saduwa a wannan lokacin. Darasinmu na yau a kan tasirin cin abincin Halal ne. An ruwaito cewa wata rana Annabi Dawud (AS) yana ganawa da Allah Ta'ala, sai ya roki Allah cewa; "Ya Ubangiji! Ina so in ga abokina wanda za mu zauna tare da shi a aljannah." Sai Allah ya saukar masa da wahayi cewa; "Gobe ka fita bayan gari, duk mutumin da ka fara haduwa da shi, to shi ne abokinka a Aljanna."
Lokacin da Annabi Dawud (AS) ya fita bayan gari,sai ya ci karo da wani mutum dauke da itace a kan kafadarsa. Sai ya tambaye shi; Meye aikin sa?" Mutumin ya ce; Kullum ina zuwa daji ne in yo itace in kawo gari in sayar da shi Dirhami daya, sai in raba Dirhami kashi uku, daya in ba mahaifiyata, daya in ciyar da iyalina, daya kuma in yi sadaka da shi ga talakawa.
Sai Annabi Dawud (AS) ya ce masa; Tabbas ka dace ka zama abokina a Aljannah! Zo mu je in nuna maka gidana. Daga yau kullum ka rika zuwa zan rika ba ka wannan Dirhamin da kake samu, ka ga kamar yadda za ka zama abokina a Aljanna, sai ka zama abokina tun a nan duniya."
Sai wannan Talakan ya ce; Ya Annabin Allah! Ai na samu matsayin zama abokinka a Aljanna ne ta hanyar wannan wahala da nake sha. In har na bar wannan aiki,to ba zan ci gaba da samun wannan matsayin ba,don haka zan ci gaba da aikina na neman halal da bautar Allah har ajali ya zo mini."
*DARASI:* Wannan kissar ta nuna mana muhimmanci dogaro-da-kai da kuma neman halal. A gefe guda ta kara nuna mana tasirin kyautata wa iyali da iyaye da raunana. Manzon Allah (S) ya ce; "Mai wahala a kan iyalinsa, kamar mai jihadi ne a kan tafarkin Allah!"