A yayin ziyarar tashi, ministan tsaron na Iran zai yi tattaunawa da takwaransa na Rasha Janar Sergey Shoygu da kuma wasu jami’an gwamnatin kasar ta Rasha.
Har ila yau, ministan tsaron na Iran zai ziyarci baje kolin makamai da ake yi a kasar ta Rasha na kasa da kasa wanda shi ne karo na 8.
Alaka a tsakanin kasashen Iran da Rasha tana da karfi ta fuskokin siyasa da tattalin arziki. Kuma a cikin shekarun bayan nan kasashen biyu suna kokarin bunkasa alakarsu ta tsaro.
A karshen shekarar 2019 an yi atisayen soja na hadin gwiwa a tsakanin sojojin Iran, China da kuma Rasha.
SOURCE: ABNA24.COM
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com