Miliyoyin Musulmi Sun Gudanar Da Juyayin Ranar Tasu’a A Duk Faɗin Duniya

Miliyoyin al’ummar musulmi musamman mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) ne a duk faɗin duniya ne suka gudanar da juyayin ranar Tasu’a, wato ranar 9 ga watan Muharram, kwana guda kafin juyayin ranar Ashura, ranar da aka kashe Imam Husain, jikan Annabi (a.s) tare da mabiyansa a Karbala.

Ita dai wannan rana ta Tasu’a, wacce aka fi saninta da ranar Biyayya Da Tsayin Daka – an ware ta ne don tunawa da irin gagarumar sadaukarwar da Abbas Ibn Ali, dan Imam Ali (a.s) kana kuma kani ga Imam Husaini (a.s) yayin abin da ya faru a Karbala ɗin.

An kashe shi ne a ƙoƙarinsa na kawo ruwa ga mata da ƙananan yara da suke sansanin Imam Husaini (a.s) bayan da aka hana su ruwa na kwanaki, inda maƙiya suka masa ƙawanya da kuma kashe shi.

A kowace irin wannan ranar dai masu zaman makoki da juyayi su kan taru a masallatai da Husainiyoyi don nuna alhini da kuma juyayin su ga abin da ya faru ga Iyalan Annabi (s.a.w.a) a Karbala.

A wannan shekarar dai ana gudanar da irin wadannan tarurrukan ne ba tare da irin gagarumin taron jama’a da aka saba yi ba saboda kiyaye kai daga kamuwa daga cutar nan ta Korona.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post