MEYASA AKE TA MAGANAR HAƊIN KAN SHIA DA SALAFIYYA (SUNNAH)?


Tare da Aliyu Samba

Meyasa kai dan Salafiyya kake ganin bazaka haɗa kai da ɗan shi'a ba?
Sabida yana zagin sahabban Annabi da sukai ɗawainiyar Addini har yazo mana yau! Indai zai dena zamu haɗa kai.
Kai kuma ɗan shi'a me yasa bazaka haɗa kai da ɗan salafiyya ba?
Saboda yana zagin iyayen da suka haifi Manzon Allah SAWA yana cewa suna wuta, kuma yana zagin AhlinSa Tsarkaka takan fifita wasu akansu! Haɗinkai zai yiwu ne kawai idan suka sauka daga wannan aƙida!

Ni kuma nace: Dukkan abubuwan da kowanne sashe yake jifan ɗan uwansa dashi zunubi ne da zai cutar da mai aikatashi kadai, baza a zargeka game da aikata zunubin waninka ba. Mushriki da ya ke zagin Allah da Annabi ya ƙaryata su da sakon da ya isa gareshi, Allah Umartar mu yayi da mu kyatata musu mu'amala, idan haɗin kai bazai yiwu ba me zai hana aƙalla a samu kyakyawar mu'amala a tsakanin ku tunda duk kun haɗu a abu mafi girma daga wannan shine kalmar shahada?

Annabi SAWA yace: bana baku labari ba, ga mafi girman zunubai, Yin shirka da Allah, wulakanta iyaye, da kuma shedar zur! (Hadisi)

Shirka fa itace mafi girman zunubi, kuma itace zunubin da Allah baya yafewa wanda ya mutu akansa, amma a tare da haka yace damu

( وَإِنْ أَحَدٌ مِّنَ الْمُشْرِكِينَ اسْتَجَارَكَ فَأَجِرْهُ حَتَّىٰ يَسْمَعَ كَلَامَ اللَّهِ ثُمَّ أَبْلِغْهُ مَأْمَنَهُ ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لَّا يَعْلَمُونَ )

التوبة (6) At-Tawba

Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to ka ba shi maƙwabtakar har ya ji saƙon Allah, sa'an nan ka isar da shi ga wurin amincewarsa. Wancan fa domin lalle ne su mutãne ne waɗanda ba su sani ba.

Meyasa bazaka yi hakan akan ɗan shia ba ya kai dan salafiyya. Meyasa bazakai haka kan dan salafiyya ba yakai ɗan shia? Shifa imani Allah bai taɓa yiwa mutane dole sai sunyi ba, shiyasa yace da Shugaba SAWA ya gaya mana cewa;

( وَقُلِ الْحَقُّ مِن رَّبِّكُمْ ۖ فَمَن شَاءَ فَلْيُؤْمِن وَمَن شَاءَ فَلْيَكْفُرْ ۚ إِنَّا أَعْتَدْنَا لِلظَّالِمِينَ نَارًا أَحَاطَ بِهِمْ سُرَادِقُهَا ۚ وَإِن يَسْتَغِيثُوا يُغَاثُوا بِمَاءٍ كَالْمُهْلِ يَشْوِي الْوُجُوهَ ۚ بِئْسَ الشَّرَابُ وَسَاءَتْ مُرْتَفَقًا )

الكهف (29) Al-Kahf

Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta. Lalle ne Mũ, Mun yi tattali dõmin azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su. Kuma idan sun nẽmi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yanã sõye fuskõki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi mũnin zama mahũtarsu.

Bayan wannan aya kuma Allah ya sake gaya mana cewa:

( لَا إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ ۖ  )

البقرة (256) Al-Baqara

Bãbu tĩlastãwa a cikin addini.

Waɗannan ayoyi sun isa su nuna mana cewa duk wanda yace shi musulmi ne kuma yayi imani da qur'ani ya san makomar aikin da yakeyi. Idan mutum baya kan taka aƙidar abune mai sauƙi, kayi taka yayi tasa, babu lallai ba dole. Allah yace da Annabi ya gaya kafurai cewa bazai bautawa abinda suke bautawa ba, suma bazasu bautawa abinda yake bautawa ba, suyi addininsu yayi nashi. A haka kuma ya zauna dasu cikin mu'amalar da sai da dayawa daga cikinsu suka musulunta saboda kyawun dabi'unsa. Baka tunanin cewa kyawawan dabi'unka da mu'amalarka a matsayinka na ɗan salafiya ga ɗan shia zai sanya ya ƙaunaceka da aƙidarka? Haka kaima ɗan shia?

Ya rage namu, ko mu haɗa kai ko kuma a cigaba da amfani da rarrabuwar kanmu ana rusa mu.

©Aliyu Samba

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post