MAWLATIY ZAINAB ALKUBRA A.S: GWARZUWAR MACE A TARIHIN MUSULUNCI



Tare da Aliyu Samba

Imam Hussaini AS shi ya Wakilci Manzon Allah SAWA a karbala, Abul Fadlil Abbas ya Wakilci Imam Aliyu AS, Alkasim Ya Wakilci Mahaifin sa Imam Hassan AS, Nana Zainabul Kubura Kuma ta Wakilci Nana Fatima. Nana zainabul kubura AS kanwa ce wajen Imam Hussaini, wacce a tarihance muka kiyaye ana kiranta Ummul masa'ib. Itace mace daya da ta dandani musiba da dacin mutuwa a duniyar musulunci fiye da kowa, bayan wafatin Kakan Ta Annabi Muhammadu SAWA, ta binne mahaifiyar ta Sayyida Azzahra data yi wafati saboda tsananin danniya da cutarwa data fuskanta daga masu da'awar mulki a lokacin, tana raye ibn Muljamin ya sari kan mahaifinta Imam Ali AS, tana raye Muawiyya ya da Ja'adatu Bint Ash'as Bin Qais ta baiwa dan uwanta Imam Hassan AS guba har ya koma GA rahamar Allah, tana raye a filin karbala Sanda hirmala ya soki Dan yayan ta Imam Hussain da kibiya wato Aliyul asgar, tana karbala a kan idonta su ubaidullahi bin ziyad, Umar bin Sa'ad da ragowar azzalumai suka sa aka farwa Abul Fadlil Abbas yayin a yayi yunkurin samo masu ruwan da zasu sha da yara, a kan idon ta shimru ibn zil jawshani ya zare takobi ya dinga saran Imam Hussaini har Sai da ya Raba kansa da gangar jikin sa, wacce MUSIBA rai zai gani a duniya da takai wannan muni.

A duk Sanda nake karanta tarihi, da na zo kan bayanin zainabul kubra kwalla ke cika min idanuwa na.

Ta zama tamkar uwa a karbala, ruhinta cike yake da hasken ahlul baiti, ta bada kariya ga Imam Sajjad AS a yayin da bayan waki'ar karbala wanda ta kansa ne hasken Ahlul Baiti ya cigaba da naso Bayan kashe dukkan zuriar dake tare da Imam Hussaini na daga maza.

Hakika ban San wata ya mace da ta nuna jarumta, sadaukantaka, juriya, da kuma hakuri irin nata ba.

Muna taya Sayyida Zainab AS ta'aziyya ahlul baiti. Allah ya girmama ladanku ya Ahlul baiti Rasulillah.

Wa sa ya alamul lazina zalamu ayya munqalibuy Yan qalibun.

©Aliyu Samba

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post