Tashar Presstv ta bayar da rahoton cewa, tun bayan da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya aike da sako ga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya aranar Alhamis da ta gabata, da ke neman a sake dawo da dukkanin takunkumai a kan kasar Iran, mambobi 13 daga cikin ambobin kwatin suka nuna rashin amincewarsu da hakan.
Rahoton ya ce kasashe 13 daga cikin kasashe 15 wato Burtaniya, Faransa, Jamus, Belgium, Chija, Rasha, Vietnam, Nijar, Saint Vincent, Grenadines, Afirka ta kudu, Indonesia, Estonia da kuma Tunisia, dukkaninsu sun rubuta wa babban sakataren majalisar dinkin duniya wasiku na rashin amincewa da wannan shiri na Amurka a kan kasar Iran, yayin da mamba ta 14 kasar Dominican ba ta ce komai kan batun ba.
Amurka dai tana son ta yi amfani da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya wajen aiwatar da wannan manufa, amma kuma hatta manyan kawayenta na turai ba su amince da hakan ba, inda ko a jiya kungiyar tarayyar turai ta fitar da bayani da ke cewa,
a halin yanzu Amurka ba ta a cikin yarjejeniyar nukiluya da aka cimmawa tare da Iran, bayan da Donald Trump ya fitar da Amurka Amurka daga cikin yarjejeniyar a hukumance,a kan hakan ba ta da hurumin yanke wani hukunci a kan wani lamari da ya shafi wani bangare na wannan yarjejeniya.
SOURCE: ABNA24.COM
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com