​Maduro: Akwai Yiwuwar Venezuela Za Ta Sayi Makamai Masu Linzami Daga Iran

Shugaban kasar Venezule Nicolas Maduro ya bayyana cewa, kasarsa na nazarin sayen makamai masu linzami daga kasar Iran.

A wata zantawa da tashar talabijin ta kasa a birnin Caracas, shugaban kasar Venezuela Nicolas maduro ya bayyana cewa, kasarsa tana nazarin sayen makamai masu linzami daga kasar Iran, domin kuwa a cewarsa babu wata doka ta duniya da ta hana kasarsa sayen makamai daga waje.

Ya ce yanzu ya umarrci ministan tsaro na kasar ta Venezuela Vladimir Padrino da ya fara tunanin hanyoyin da za a iya kulla irin wannan ciniki tare da kasar Iran, da kuma yadda za a aiwatar da shi.

Maduro ya ce, sakamakon aikawa da kayayyakin aiki na gyaran matatun mai da Iran ta yi zuwa ga Venezuela, a halin yanzu kasar ta fara shirye-shiryen gudanar da aikin gyaran matatun mai na kasar, wanda zai taimaka mata wajen kawo karshen matsalar man fetur a cikin gida, har ma da kasashen da suke samun mai daga gare ta a cikin kasashen latin Amurka.

Kasar Venezuela dai ita ce kasa ta farko wajen yawan danyen man fetur a duniya da yake kwane a karkashin kasa, wanda hakan ne yasa manyan kasashen duniya ke hankoron yin kutse a cikin kasar domin kwasar garabasa, amma gwamnatin kasar ba ta ba su hanyar yin hakan ba.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post