KHUDUBAR SAYYIDAH ZAINAB (S.A) GA MUTANEN KUFA !!!


* MA'ASUMIYAH NIGERIAN NEWS UPDATES *
Sayyida Zainab (S.A) na tare da Imam Hussaini (A.S) a filin Karbala, kuma ita ce babba cikin iyalan Ma'aiki (S) da aka keta alfarmar su.

Jahiz ya kawo cikin littafinsa me suna (Albayan Wal-Tibyain) , daga baban Ishaq, daga Khuzaimatal-Asdiy cewa;
Na shigo Kufah a shekara ta 61 (B.H) sai na tarar an tattaro Hussaini Bn Aliyu da zuriyarsa daga Karbala zuwa ga Ibn Ziyad a Kufah. Na ga matan Kufah a tsattsaye a wannan lokaci, kuma na ga Zainab Bnt Aliyu (K.W). Wallahi ban taba ganin mai kafin harshe kamarta ba, tamkar dai (furucin) na fitowa ne daga harshen shugaban muminai.

Ta nusar da mutane cewa suyi shiru, duk rayuka su kayi shiru sannan tace;
" Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga shugaban Manzanni, bayan haka;
Yaa ku mutanen Kufah, yaa ku ma'abuta ha'inci da saba alqawari? Lalle misalinku shine kamar misalin;
" KAMAR WACCE TA WARWARE ZARENTA NE BAYAN TUFKA, YA ZAME WARWARARRE. KUNA RIQON RANTSUWOWINKU DOMIN YAUDARA A TSAKANINKU ."
(Nahli:92).

Ku saurara, lalle daga cikinku akwai masu yabon Kansu da abinda ba su dashi, suna furta abinda ba shine cikin zuciyarsu ba.
Ku saurara, abinda kuka dauka (na zunubi) ya munana. Eh, wallahi kuyi kuka mai yawa kuma kuyi dariya kadan. Haqiqa kun tafi da dukkan wani aibu da illar da ba za ku taba wanke su ba har abada!
Lalle kun jibinci kashe dan goshin cikamakin Annabawa, ma'adanin Manzanci, magangarar hujjojinsu, kuma shugaban samarin Alannah. Kaicanku yaa mutanen Kufah, lalle abinda zukatanku suka riya muku ya munana. Fushin Allah ya tabbata a kanku, kuma za ku dawwama cikin azaba.

Ba ku san tsoka ce daga Manzon Allah kuka sare ba? Ba ku san jini ne daga gare shi kuka sheqar ba? Ba ku san cewa da karamarsa ku kayi fito-na-fito ba?
" HAQIQA KUNZO DA WANI ABU MAI GIRMAN MUNI. SAMMAI SUNA KUSA SU TSATTSAGE SABODA SHI, KUMA QASA TA KECE, KUMA DUWATSU SU FADI SUNA KARYAYYU ".
(Maryam:89-90)

Zamuci Gaba insha Allah

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post