A karshe-karshen jawabin da ya gabatar a gurin taron cika alkawuran zaman makokin Ashura na shekara mai kamawa da aka gabatar a Sakkwato, Sayyid Badamasi Yaqoub ya yi gajeren bayani dangane da halin da su Malam (H) suke ciki kamar yadda aka bukata. Taron wanda yan'uwa na da'irar Sakkwato suka shirya tare da gudanarwa a Yau Litinin 3/8/2020 a Husainiyya Imam Mahadi ATF dake Sakkwato.
Sayyid Badamasi ya bayyana cewa, “Malam (H) yana nan kamar yadda aka sani, yau lafiya gobe ciwo, wannan kuma ba abinda zai baiwa yan'uwa mamaki bane domin wadannan da suke cigaba da tsare shi guba suka bashi, haka kuma harsashin da suka harbesa dashi yana dauke da guba ne, amma dai kai ba zaka iya sani ba, idan ba shi Malam din ne ya gaya maka ba.”
Ya cigaba da cewa, “da zaka ga su Malam a ido da kuma jin maganarsa zaka ji su duk tsaf, amma da zaka tambayi su Malam da cewa, yaya jiki ? To idan kai ahalin ya gaya maka ne zai gaya maka, idan ko ba ahalin ya gaya maka bane zai ce maka lafiya lau ne.”
Ya kara da cewa, “na san a bayabayan nan baifi sati biyu ba, shugaban kurkukun da su Malam suke tsare, ya sa an kwashe duka magungunan da su Malam suke amfani dashi, shi da Malama, wanda kuma da aka tambayeshi dalilin hakan hujjarsa ana kawowa su Malam magunguna ba tare da saninsa ba.”
A karshe Sayyid Badamasi ya karkare jawabin nasa tare da fatar cewa, “Bi'izinillahi Allah (t) zai mana tagomashi da ganin karshen wadannan azzalumai, haka kuma duk yadda suka kai ga son su ga bayan Malam Insha'Allah ba zasu yi nasara ba, domin kuwa da suna da hankali ai su sun kashe Malam ne, amma Allah ya raya shi, saboda haka Allah (t) da ya raya shi bayan sun kashe shi, shine zai kubutar dashi ?.”
–Bilal Nasir Umar Sakkwato.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
#FREE_ZAKZAKY