Labari Da Dumi-Duminsa : Kwamishinan ‘Yan Sandan Da Ya Kashe ‘Yan Shi’a 26 A Kano Ya Mutu




AIG RABIU YUSUF YA MUTU

Da safiya yau Asabar ne aka sanar da mutuwar AIG Rabiu Yusuf wanda yake Zone 14 Katsina.

CP Rabiu Yusuf shine Kwamishinan 'Yan Sanda na jihar Kano a shekarar 2016 har 2019. A lokacinsa ne aka yi Waqi'ar Ashura ta 2016 a Kano, inda yan sanda suka sa kayan yan daba suka sassari yan uwa a wajen muzahara, suka kama kusan 100 suka kai su kotu.

A lokacin sa ne aka yi Waqi'ar Tattakin Kano 2016, in da suka rutsa yan uwa masu Tattaki na yankin Kano su ka yi ta kisa.

CP Rabi'u Yusuf da kansa ya je wajen da bindigar sa pistol a hannu. Wasu yan uwa da aka kama sun ce da hannunsa yake harbi. Ya kashe yan uwa kimanin 26 inda ya kwashe gawarwaki mafi yawa yasa aka je Hayin Kalebawa cikin dare aka binne su a boye. A wannan waqi'a ne suka kama yan uwa 58 mafi yawansu masu harbi a jiki. Aka tsare su tsawon wata 7 a kurkuku.

Da shekara ta zagayo, ya sake haddasa Waqi'ar Tattakin 2017 inda aka kashe yan uwa 4 ciki har da Shaheeda Hussaina Dauda Nalado. Aka kuma kama yan uwa kusan 15 aka kaisu kotu.

Bayan waqiar bai saduda ba. Ya ci gaba da tsanantawa yan uwa. Idan za a yi muzahara ya kan zauna da wakilan yan uwa ya ce shi bai yadda a yi muzahara ba. Idan an yi zai turo 'boys' su yi abin da ya dace. Haka dai yan uwa su ka yi ta fama dashi har aka dauke shi a shekarar 2019.

A yau dai Allah Ya dauke shi. Ya mutu bayan gajeriyar jinya. Allah ya yi masa hukunci da aikin sa.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post