Kwamitin Tsaro Na MDD Ya Ki Yarda Da Tattauna Bukatar Amurka Na Tsawaita Takunkumi Akan Iran

Shugaban kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya, wanda yake wakiltar kasar Indonesia Dian Triansyah Djani, ya bayyana cewa; “ Ba a sami cimma matsaya ba a tsakanin mambobin kwamitin tsaron dangane da bukatar Amurka na a tsawaita wa Iran din takunkumi, don haka ba za dauki wani mataki akan wannan batun ba.”

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya ambato shugaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniyar yana cewa; Na sami wasiku masu yawa daga kasashen da su ke mambobi, abinda ya fito fili a gare ni shi ne cewa kasa daya tilo take da ra’ayin da ya sha banban akan wannan batu, amma sauran duk ra’ayinsu daya.”

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai ministan harkokin wajen Amurka ya gabatar wa da kwamitin tsaron bukatar a kara tsawaita takunkumin hana saye da sayar da makamai akan Iran.

Kasashen mambobi a cikin kwamitin tsaron sun yi watsi da bukatar ta Amurka ne saboda hakan yana cin karo da kudurin Majalisar Dinkin Duniya.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post