Daga Imam Ja'afar Bn Muhammad, daga babansa daga kakansa (A.S) yace, Imam Ali (A.S) yace: " GA KOWANNE MUTUM MUSULMI YANA DA ABOKAI UKU; (i)-ABOKINSA DAKE CE MASA, NI INA TARE DAKAI A RAYE KAKE KO A MACE; SHINE AIKINSA. (ii)-ABOKINSA DAKE CE MASA; NI INA TARE DAKAI HAR ZUWA QOFAR QABARINKA SANNAN NA BARKA; SHINE 'DANSA. (iii)-ABOKINSA DAKE CE MASA, NI INA TARE DAKAI HAR KA MUTU, TO ITA CE DUKIYARSA,IDAN YA MUTU SAI TA ZAMA TA MAGADANSA ". Al-Kisaal J:1, SH:112.
ABIN LURA =============== Abinda kawai zai amfanar da mutum bayan rayuwarsa shine Imaninsa da kuma aikinsa. Kamar yadda Allah (T) ne ke cewa: " ALLAZEENA AAMANUU WA'AMILUS-SAALIHATI, 'DUUBAA LAHUM WA HUSNU MA'AAB "==" Wadanda sukayi imani kuma suka aikata aiki mai kyau, farin ciki ya tabbata a gare su, da kuma kyakkyawan makoma ". Ra'ad :29. ALLAH YA GYARA MANA AYYUKANMU.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Tunatarwa