Ko Kun San| Yawan shan Ababe Masu Zaki Suna Haddasar Da Ciwon Hakori??




Hakan ka iya zama sanadin kamuwa da cutar nan ta kogon hakuri.
Wadanda ababe masu zaki suka fi yiwa barazanar lalacewar hakuri, sune; yara kanana domin a lokacin hakoransu ba su da karfi, sannan kuma garkuwar jikinsu ba ta da karfin fada da kwayoyin cuta yanda ya kamata.
Yawan sayawa yara biskit, minti, bobo, kolon dadi, cakuleti da sauransu ba gata ba ne ba, illa ce babba wacce take haifar da lalacewar hakoran yaranmu.
Don haka a mainakon haka sai mu rika saya musu kayan marmari, irinsu: kankana, lemu, kwakwa, gyada, ayaba, gwanda, abarba, tuffa da sauransu. Wadannan suna taimakawa sosai wurin hana lalacewar hakoran yaranmu.

Abubuwa masu muhimmanci:

Yana da kyau, mu koyawa yaranmu kuskure baki duk bayan sun ci wani abu komai kankantar shi, hakan zai taimaka wurin samun ingantacciyar tsabtar bakinsu, da hanasu kanuwa da cutukan hakori.

Naku har kullum.
-Dent FS Modibbo Gozaki
-modibbogozaky@gmail.com
-08063607225
-07067703588
-08113132445

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post