Ko Kasan Yadda Ta Kaya Tsakanin Dattijon Arziki, Sheikh Sale Lazare Da Yan Shi'an Buhari A Iran Kuwa??


Yan raaf wato Shi'ar neman tuwo sun kwashi kashin su a hannu, kai dai karanta kasha labarin.

To, lokacin da Kaid ya fito, mutane suna dan tashi suka dan yi maganganu zuwa gare shi kafin ya yi jawabi. To, ni ma na dan tashi na yi gaisuwa, na ce ni daga Nijar nake, amma ina iya cewa daga Nijeriya nake, a matsayin daya daga cikin hannun (Almajiran) Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), kuma lallai halin da yake ciki yana da tsananin bukatar adduarku ya Sayyid! A takaice dai abin da na dan gabatar ke nan.
To, lokacin da Kaid zai yi magana, bai manta da wannan maganar ba, sai da ya bi ta kanta, ya ce Allama Sayyid Ibraheem Zakzaky, halin da yake ciki muna sane da shi, muna jin sa a cikin ruhinmu. Amma yadda yake da bukatar adduarmu, mu ma muna da bukatar adduarsa.
To, wannan bayanin da Sayyid Khamenei ya yi mana, sai ya warkar da ni game da damuwar da nake da ita na cewa, babu wani mutumin Malam ko guda da ya zo wannan taron, sai ni da ba kowan kowa ba makararre. Sai na ji wannan magana ta Kaid ta warkar da ni. Cewa su ma suna da bukatar adduar Malam (H). A nan na sake duba girman sakacin da muka yi na rikon wannan Jauharin da Allah ya ba mu kyautar sa. Ashe har yau ba mu fahimci waye shi ba. Wannan ya sa na kara nitso a cikin wannan lamarin. To, kuma na dauki alkawari tsakani na da Allah cewa, wannan sako na Kaid, insha Allah sai na isar wa da Malam (H) da shi. To, yaushe zan isar kuma ta ina? Alhamdulillah na sauke wannan nauyin. Na isar da shi baki da baki ga su Malam (H). Wannan ke nan.
Sai aka zo aka ci gaba da taro. Rana ta farko an yi magana a kan abubuwan da ke damun Musulunci a wannan zamanin, firka ta Takfiriyya da firka ta Shiancin London. A kan su aka yi magana, aka ce a lura da wadannan ababe guda biyu, sune babbar matsalar Musulunci a wannan lokaci. Hadarin da ke tunkarar Musulunci, babu kamar wadannan firkoki guda biyu. Takfiriyya da yan Shiar London (su Yasir Habib ke nan). In muka duba wadannan kungoyoyi guda biyu suna da salo iri daya. Suna amfani da abin hannu don farauto zukatan mutane, kuma yanadam bayi ne na abin hannu.
Mai bayani yana kare jawabinsa, sai wani yaro ya tashi, daga nan Nijeriya ya zo. Sai yake cewa, lallai akwai kari, Harka Islamiyya a Nijeriya ita ma a kara da ita. Ita ma matsala ce a kan addini. Ya ce su da suke Nijeriya, su suka san hadarin da ke cikin wannan abin da ake cewa Harkar Musuluci din, don haka ita ma a saka da ita. Ya ce, saboda Harkar Musulunci ta jawo wa Shianci bakin jini, ba kawai a Nijeriya ba, har a dukkan Afirka. Don haka yana rokon Jamhuriyar Musulunci ta yanke gudummawar da take ba Harka Islamiyya. Wato yana neman Iran ta bar raya Harka Islamiyya da kudi.
To, da ya kare magana ya zauna, duk wanda ya yi magana a kan yi masa taaliki na karin bayani, ko gyara, ko wani abu da ya yi kama da hakan, amma shi ba a masa ko daya ba. To, a lokacin ne na daga hannu na dauki abin magana. Na ce jikana ko na ce dana ya yi magana a kan abin da ya shafi Harka Islamiyyah, ko Nijeriya, amma ban ji an ce komai ba. Don haka na dawo da maganar. Na ce, cikin abubuwa da ya fada, musamman a kan Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), ina so kowa ya kwana da sanin cewa, Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya dauki Shianci a matsayin Akida, Addini kuma ibada, wanda a wajen Allah (T) kadai ake neman sakayyarsu. Sabanin wadanda suka dauki Shianci a matsayin tarkon farauta, ko hannun jarin neman abin duniya. Na ce kodayake ni daga Nijar nake, amma in ma na zo ne daga Nijar, to amma ni na cikin hannun Sayyid Ibraheem Zakzaky ne. Abin da ya koya mana shi ne tsayawa a kan manufa kyam da kuma daukar nauyin kai da kai, mu yi wa kanmu, mu yi wa wasu, ko da kuwa makiyanmu ne. Don haka shi yake aikatawa.
Na ce, kodayake shi wannan yaro ya yi maganarsa ba tare da kawo misali ba, amma ni bari in ba ku misalin cewa Malam (H) ya tsaya a kan kafarsa, kuma yana ma kansa ne, ya yi wa wani. Na ce, a dabiar Malam da ya saba, makwabtansa a unguwar da yake zauna a Gyallesu idan watan Ramadan ya zo alummarmu suna da tsananin bukatar abin da za su yi bude-baki da shi, saboda an talautar da mutane da gangan, to Malam yakan raba abinci ga makwabtansa. Abincin da yake rabawa ba yan kunshe-kunshe a ledodi ko a tsumma ba ne, ba wai kwano ake aunawa a zuba a ba mutum ya tafi ba, aa, tona-tonai (buhuna) ake saya na shinkafa, masara da gero da sauransu a raba wa mutane.
To, sai ga wannan abu da ya zo ya faru, na cewa an kashe, an kona, an yi abin da aka yi an rusa, shi ma Malam din kansa an tafi da shi, a lokacin ba mu sani ba a raye yake ko a mace, kuma ba sa bari a je wajensa a farko. Sai Allah ya sa dangin Malam na jini suka samu damar kai masa ziyara, gab da Ramadan. Da suka je, sai Malam ya ce, to masha Allah, na yi murnar zuwan nan naku, don ina da abin da ya dame ni; ga Ramadan ya zo, dan alherin da ake wa makwabtana a Gyallesu, to bana ma kar a fasa. To, da yake akwai Kanin Malam Shakikinsa, Sayyid Badamasi, sai ya ce, to Akramakallahu, cikin wadanda muka san ana ba wannan alherin, akwai wane da wane, a saninmu wadannan mutanen bayan an rusa gidanku, an yi abin da aka yi suna cikin wadanda suka yi wasoson kayan gidan. Shin yanzu in mun tashi rabawa, har da su? Ya ce wa Malam, musamman ma akwai wane, wanda ya yi batanci da miyagun maganganu a kan ku a Media, wanda bai kamata ba, kuma mun san har da shi aka yi abin da aka yi. To, yanzu su ma har da su za a ba? Shi fata yake a ce masa kar a ba su. Amma bude bakin Malam sai ya yi murmushi ya ce masa idan kun tashi rabon ina muku wasicci da umurnin cewa a fara ta kan wadannan. Duk wajen sai suka yi salati. Na ce, to wannan shi ne Malam Zakzaky (H).

*Na ce, wannan jika nawa ko dana, ya yi rokon cewa ku daina tura wa* 

*Harka Islamiyya kudi* *baku ce komai ba.*

*To, ina so yanzu ku fito fili ku fada wa duniya, shin ku kuke daukar nauyin Harka Islamiyya?* 

Ni a sanina ba ku ba ne. A sanina ba kwa daukar nauyin Harkar Musulunci a Nijeriya. Ina da hujja. Na ce duk da ina Nijar, amma na san komai. A sanina a Zariya ko a wani gari a fadin Nijeriya da wajenta, ban san cewa kun gina wa Malam Zakzaky (H) aji guda daya na makaranta ba, ballatana makaranta cikakkiya. 

To, amma wannan bangare yan kadan da ba ta amfanar ba, kuma ba za su taba amfanarwa ba har abada, kun gina masu manya-manyan gine-gine, kun gina masu benaye, ba abin da suke kawowa sai tsegumi.
To, mu abin da Malam ya dora mu a kai shi ne dogaro da kai, da tsayawa kyam a kan addini, ba jiran wani ya yi mana ba. Ko da kun ga mun zo nan gare ku, Iran, 

*to ba mu zo don Dalolinku ba, abin da ya kawo mu shi ne; akwai wasu ilmummuka da sirrori da Imam Ruhullah Khumain (KS) ya tafi ya bar maku, su kuka gada, to su muke tahowa gare su don mu caza batirorinmu zo mu amfana da su, mu je mu amfanar. Abin da ke kawo mu ke nan, ba neman Daloli ba.*

Na ce to, jikan nawa ya yi nasa rokon ba ku ce masa komai ba, *amma ni ma ina da nawa rokon. Nawa kuwa shi ne; ina roko ga wannan Kasa Mai Albarka, tun daga Kiyadarta har Hukumarta, har Shaab dinta Masu Albarka (Allah ya kara kare su), dukkan wata gudummawar kudi da suke tura wa Afirka baki daya a dakatar da ita.*

 To, a lokacin sai na ga yan Afirka da ke cikin zauren suna jujjuya idanu. Sai na duba na ce, to ga dukkan alamu maganata ta yi nauyi ga yan uwana yan Afirka, to bari na sassauta. 

*Ina roka ga cewa a dakatar da dukkan abin da ake tura wa Afirka da sunan daam ko tamwil. Don Allah a yi wannan ko da na shekara 10 ne.*

 Na ce, don ta bayyana ga kowa su waye yan Shia na hakika, su waye yan kasuwanci da Shia! Na ce abin da nake roka ke nan. Wabillahit Taufik.

Malam, ina kare magana, sai wani yaro daga Ghana ya zabura, ina rike da sunan yaron sunansa Muhammad, shi bai nemi izinin kowa ba, ya zabura kawai ya tashi tsaye, Allah ya masa murya da sauti na magana, kuma ya iya magana da Larabci sosai. Ya ce; Dattijo, Baba, ka cece mu, Allah ya saka maka da alheri. Ya ce; Don ba don kai ba, wannan zaure da muke cikin sa da yanzu-yanzun nan da muke ciki ba da jimawa ba Allah sai ya zubo mana azaba saboda an taba Waliyyinsa, Sayyid Ibraheem Zakzaky! Ya ce; Afrika gaba daya wa muke da shi sama da Malam Ibraheem Zakzaky? Ya yi kuka. Yana magana ana lallashin sa. Da kyar aka shawo kansa.
To, a lokacin dole shi Shugaban zaman ya dauki abin magana ya ce; Zakzaky Allah ya kwato shi, ba mu da bukatar sai an fada mana ko shi waye. Ba mu da bukatar sai an tunatar da mu ayyukansa da gudummawarsa da kuma himmarsa. Ya ce; Lamarin Zakzaky kamar rana ce a tsakiya, ba ta bukatar wani bayani. Fatanmu dai Allah ya gagauta kwato mana shi. A nan dai wannan maganar ta kare.
Ran Litinin aka yi wannan, to ranar ban fita ba saboda jikina akwai dan nauyi, kuma akwai sanyi kankara na zuba. Sai ranar Talata na fita, na yi ta harba ido, shi wannan yaro ban gan shi ba. Sai ranar Laraba na yi magana, na ce kai ni fa yaron nan da ya yi maganar nan ban gan shi ba. Sai aka ce min ai tun jiya Talata an mai da shi Nijeriya.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post