*
Mun buqaci kawo wannan Hadisi ne domin kawar da Shubhar da ake kawowa na cewa wai Abubakar shine mai yiwa mutane sallah yayin JINYAR Annabi (S. A. W. W).
*
Wannan Shubhar da su ke kawowa sai su ka dauke ta wai a mstsayin dalilin da ke nuna cewa Abubakar shine zai ga ji Annabi a bayansa.
Bari mu kawo Hadisin don mu nazarce shi.
*
Bukhari ya riwaito cewa, Umar Bn Hafsin Bn Ghiyas ya ba mu labari yace, banana ya ba ni labari yace, A'amashu ya ba ni labari daga Ibrahim, daga Aswad yace, mun kasance a wajen A'isha sai mu ke tattaunawa game da mai da hankali kan sallah da kuma girman ta sai ta ce,
Yayin da annabi ya ke rashin lafiya wanda ya rasu a cikin ta sai lokacin sallah yayi, aka yi kiran sallah sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace:
" KU UMARCI ABUBUKAR YA YIWA MUTANE SALLAH. "
Sai aka ce masa, Abubakar mutum ne mai tattausar zuciya Idan ya tsaya a gurin da kake tsayuwa ba ya iya yiwa mutane sallah. Har sau uku yana maimaitawa (na cewa a umarci Abubakar ). Sai yace :
" KU DAI KAMAR MATAN ANNABI YUSUF KU KE " (wajen jayayya ), KU UMARCI ABUBUKAR YA YIWA MUTANE SALLAH ".
Sai Abubakar ya fita yana sallah sai Manzon Allah (S. A. W. W) ya ji sauqi sauqi, sai ya fita yana tsakanin mutane biyu (Abbas da Imam Ali) kamar ina kallonsa yayin da qafafunsa ke sharar qasa saboda jinyar ta sa.
Sai Abubakar ya yi nufin ya dawo baya ( don Annabi ya wuce gaba ). Sai Annabi yayi masa nuni da cewa :
" KA TSAYA A WAJEN KA (don cigaba da yiwa mutane sallah. "
*
Sai aka kai shi (Annabi ) ya zauna a gefensa (Abubakar ). Aka cewa A'amashu, Annabi ya kasance yana Yin sallah ne Abubakar ya na koyi da sallar sa, su kuma mutane suna koyi da sallar Abubakar?
Sai A'amashu ya gyada kansa (kamar Qadangare ) yace eh. "
*
( Bukhari, Hadisi mai lamba 664 ).
*
======== NAZARI ========
Idan mu ka nazarci qarshen Hadisin Abinda ya ke nuna mana shine, da Annabi (S. A. W. W) ya fito shi ya jagoran sallar, Abubakar kuma yana yin koyi da shi, sauran mutane suna koyi da Abubakar.
Kenan Annabi ne ya jagoranci sallar ba Abubakar ba. Sannan kuma a lokacin da Abubakar din ya fara sallah babu Imam Ali a cikin sallar, domin suna tare da Annabi (S. A. W. W).
*
========= TAMBAYA =========
*
(1)- Shin, Idan aka ce Annabi yana sallah Abubakar kuma na yin koyi da shi to, waye limamin a cikin su?
*
(2)- Idan ka ce Annabi ne limamin to, Abubakar ya zama mamu Kenan?
*
(3)- To, Idan Abubakar mamu ne, me yasa sauran mutane ke yin koyi da mamu yayin da su ke sallah da limamin?
*
(4)- Shin, da ma ana samun limamai biyu ne cikin sallah guda?
*
======== GASKIYAR MAGANA =======
*
Abubakar bai jagoranci sallah yayin da Annabi ke raye ba. Wannan guda Dayan (1) ma da ake magana a kai qirqirar masu qirqira ne, kuma sun warware kayan su ta hanyar fitowar Annabi (S. A. W. W) da yin sallar sa ga mutane yayin da Abubakar din ke tare da su.
Saboda haka batun jagorancin sallah sa ma ba ta inganta ba ballantana a dauke ta a mstsayin wata hujjah na Khalifancin sa.
*
FREE SAYYID ZAKZAKY (H) !!!
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com