Rahotannin sun ci gaba da bayyana cewa jami’an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla sannan kuma suka yi harbi da harsasai masu rai akan masu zaman juyayin wadanda suka hada maza da mata da kuma kananan yara.
An nuna cewa akalla mutum daya yayi shahada sannan kuma wasu da dama sun jikkita sakamakon wannan harin da jami’an tsaron suka kai.
Shi dai wannan zama ana gabatar da shi a fadin Nigeria da sauran kasashen musulmi na duniya.
A ko wacce shekara a cikin watan farko na Muharram al’ummar musulmi suna juyayin abin daya faru na kashe jikan Manzon Allah[SAWA] watau Imam Hussain[AS] a shekara ta 61 bayan hijirar Manzon Allah[SAWA].
SOURCE: https://harkarmusulunci.org/
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com