A cikin bayanin da ma’aikatar ta fitar, ta bayyana cewa jami’ai masu gudanar da ayyukan tsaro na asiri na kasar ta Iran, sun samu nasarar damke mutane 5, wadanda suke gudanar da ayyuka ga hukumar leken asiri ta Amurka CIA, da kuma kungiyar leken asiri ta Isra’ila MOSSAD.
Bayanin ya ce, bangarorin da wadannan mutane suke tattara bayanai a cikinsu suna mika wa CIA da MOSSAD, sun hada da ma’aikatar harkokin waje, ma’aikatar tsaro, ma’aikatar kula da kamfanoni da masana’antu, da kuma hukumar makamashin nunkiliya ta kasar.
Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, mutanen suna amfani da wasu hanyoyi ne masu sarkakiya wajen aikewa da bayanan nasu, amma duk da haka da taimakon Allah, an samu nasarar gano su, kuma aka cafke su.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake gano ma’iaktan hukumomin leken asiri na Amurka da Isra’ila a cikin kasar ta Iran ba, inda ko a kwanakin baya an zartar da hukuncin kisa a kan Mahmud Musawi majd, wanda ya rika bayar da bayanan sirri ga hukumomin leken asiri na Amurka da Isra’ila kan janar Kasim Sulaimani da wasu manyan jami’an soji na Iran da suke aikia matsayin mashawarta kan harkokin tsaro a cikin kasashen Syria da Iraki.
SOURCE: ABNA24.COM
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com