Yanar Gizo wani guri ne da ya kasance mutane da dama suna mu'amala dashi, sai dai manufofinsu ne kawai suka bambanta.
Wasu sukan shige ne kawai don nishadi, musamman 'yammata da samari.
Wasu kuma suna amfani da shi ne kawai don suga abubuwan da ke gudana a qasa, yayin da wasu kan shige shi don kawai ace su ma suna shigarsa.
To, a irin wannan manufar ce mabambanta ya kasance nima na shige da wata manufa.
Babbar manufana ta mu'amala da yanar Gizo (social media) shine kawai don na yada aqidar gidan iyalan Ma'aiki (S.A.W.W) wacce miyagun mutane na gidan Banu Umayyah suka buye tare da jirkitata.
Alhamdulil-Lah, shigata tayi matuqar amfana ta tare da amfanar da wasu.
Na'am, sau da yawa wasu kan ce min rashin abin yi ne yasa ni yin abinda nake yi, yayin da ni kuma ke musu fassarar marar sanin abinda suke yi, domin su ba su da manufa a rayuwarsu.
Mu'amalata da wannan kafa ya ilimantar dani abubuwa masu yawa, tare da taimaka min wajen isar da saqon harka islama.
Ba na manta wani rubutu da nayi a shafin mu na (MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS), wanda ya isa zuwa kan mutane sama da dubu dari (100,000), ga sharri marar adadi tare da goyon baya.
Nayi rubutun ne kan abin bautar wawayen Nigeria, wannan yayi sanadin samu albarka daga bakin salihan Bayi, da kuma tsinuwa daga zuriyar Alhanzir.
Kiran lambata kuwa babu adadi.
Dole na nuna farin cikina kasantuwar amsa kiran (phone) da nayi na wani malamina me suna; M.I GAMAWA, shahararren manubuci ne a jaridar ALMIZAN wanda mutane da dama na shauqin fitowar jaridar kawai don su ga rubutunsa.
A qarshe ina godiya ga abokai masu farin ciki da ganin rubutunmu a shafin (MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS).
Ku kasance tare damu a shafin don qaruwar Mu Da ku !!!
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com