"Aikin da ke gaban masu neman kawo sauyi ba 'karami ba ne! Kwanan nan muna Lebanon, mun gana da Sayyid Hassan Nasarallah, mun zauna mun tattauna har wajan awa 4, abubuwan da muka tattauna suna da darussa da yawan gaske! Sidi Abba AliyuAmma daya daga ciki (wanda kuma ya dace da maganar da muke yi yanzu) shi ne abin da ya fada, ya ce; Shin yanzu inda za a ce masa "Sayyid Bisimillah, ga Lebanon nan (an damka muku) ku gudanar da nizamin Musulunci" ya ce; Lallai shi ba zai karba ba.
Ya ce saboda ba su da (wadatattun) ma'aikatan da za su iya gudanar da tsarin.
Sai na ce; Tooh, ku ma kenan fa!! Ballantana su mu! Yanzu da za a ce; "Ina Shiite ('yan Shi'a)? Ku ne ku ka fi gaskiya da rikon Amana, Ga Nijeriya nan (an ba ku ku mulketa)! Rikita-rikita!!!
Amma lokacin juyin Musulunci na Iran Imam (QS) yana da wannan Imkaniyya din, akwai isassun wanda za su iya gudanar da abubuwa".
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a jawabin rufe Daurar 'yan uwa Mata a 2015.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Jawaban Sheikh Zakzaky