IMAM HUSSEIN DA KARBALA



Rigimar Karbala ba tsakanin Imam Hussein (as) da Yazid bn Mu’awiya ba ce. Rigima ce tsakanin masu kudi da mulkin da suke neman a koma al'adun jahiliyya na zalinci ko da da sunan musulinci da kuma masu neman a bawa kowa yanci don ci gaban musulinci. Ci gaban musulmi shi ne ci gaban musulinci. Kafa daula ba ta da amfani matukar a na ci gaba da zalinci. Meye amfanin irin Shari’ar Zamfara da talauci kawai ta karawa mutane?

Ba rigima bace akan mulki kamar yadda wasu suke zato. Ko ni da nake dosanon Ahlel Bayt ta hanyar sufanci mulki bai dameni ba balle kuma Imam Hussein da aka haifa a gidan Annabta. Abin da mulkin zai yi shi yafi damunsa ba shi kansa mulkin ba.


Imam Hussein, babansa Imam Ali da kakansa Annabi Muhammad, duka sun yi yaki ne don ceton al’umma daga hannun azzaluman “elites” din larabawa da mafi yawansu daga Banu Umayya suke.

In ban da banbancin tunani da nake da wasu, ni a ganina Karbala zamu tuna da ita ne a matsayin wata babbar nasarar da Sayyidi Hussein ya yi, ba wai zaman makokin damuwa da faduwarsa ba. Babu wata nasara a musulinci tun bayan “Fathu Makka” da ta kai “Waqi’atu Karbala”. Ita ta canja tarihin musulinci baki dayansa.

A cikin kowace rashin nasara ta dan juyin-juya-hali ake gane nasararsa. Wannan tasa yan kadan daga Annabawa ne ba’a kashesu ba. “Spartacus” sun yi nasara ne a cikin rashin nasara. “300 Spartans” sun yi nasara a lokacin da ake zaton faduwarsu. Haka duk tarihin juya-hali yake. Tarihi shi yake nuna nasara a zamanin da ake ci gaba da alhini.

Nasarar kowane mai kwato yanci a matakin farko ba ta kafa daula bace. Nasararsa na cikin budewa masu gaskiya hanya domin su dora wajen gano hakkinsu kuma su yi nasara a nan gaba. Wannan ne abin da Imam Hussein ya gano har yace ba zai hakura ba har sai ya fita, duk da wasu suna ganin bai dace ba.

Da a ce Imam Hussein ya kafa daula tamkar sauran sarakuna, da sai dai mu karanta tarihinsa kawai a litattafai. Amma “rashin” nasararsa ta janyo duka muka san shi a tsakanin jinin jikinmu. Yan Shi'a sun yi gaskiya da suka ce “Kowace rana Ashura ce, kowace kasa Karbala ce”. A ko da yaushe zamu fita kwato yancinmu, a ko ina zamu iya nemar hakkinmu. Ba abinda ya shafemu da abinda zai faru damu don za’a tuna damu tamkar Hussein a Karbala.

Daga Hussein duka juyin-juya halin da ya kafu a musulinci ya samo asali. Da kan Hussein Banul Abbas suka yi wa Banu Umayya zanga-zanga har suka barar da su. Da kan Hussein Daular Fadimiyya suka yi wa Banul Abbas tawayen zalincin da suke. Da Hussein aka kafa duk wata gwamnati a musulinci da ta yi karko, daga Usmaniyya zuwa Iran (a zamanin Shah da na Khomeini).

Banu Umayya sun so su karar da jinin Manzon Allah ta kan Hussein amma sun yi a banza. Sun kasheshi amma sun bar sunansa. Su yanzu da suka yi kisan suna ina? Waye ya san su? Amma a tsakanin kowane gidan musulmi  akwai sunan Husseini da yan gidansu. Kakaf sai ka zagaye unguwa da kyar zaka samu Yazidu ko babansa Muawiya.

Su ba Husseini suka so kashewa ba, Manzon Allah da danginsa suka so kararwa. Duk sarakunan banu Umayya kamar yadda Ibn Kathir ya fada, in banda Muawiya na biyu da Umar dan Abdulaziz, “nawasib” ne,  sun tsani ahalin Annabi saboda sun lalata musu mulkin jahiliyya. Ka auna ka gani : Abu Sufyan ya kori Manzon Allah, Muawiya ya yaki Imam Ali, Yazidu ya kashe Imam Hussein!

Ba rigimar addini bace kawai, kamar yadda mutane dayawa suke zato. Kafin musulinci Banu Umayya suna shugabantar “capitalists” (yan jari-hujja) da suke Makka ne. Addini ba damunsu ya yi ba matukar ba zaka taba kasuwancinsu na zalinci ko mulkinsu na danniya ba. Laifin Manzon Allah a gunsu shi ne yace a dinga biyan hakkokin mata da aka dauka ba mutane ba, bayi da raunana da ake zalinta, hana zalincin riba (interests) da kuma cewa duka al’umma matsayinsu daya a gurin Allah.

Banu Umayya ba bautar Allah daya ce tafi damunsu ba, zamanin da suna Makka a jahiliyya sun bawa kowa yancin addini matukar ba zai taba musu harkokin zalinci ba. Suna bautawa Lat da Uzza, amma a Ka’aba akwai allolin Greeks (Hubal = Zeus), Egypt  (Nasra = Isis), kai har da na Jesus da Virgin Mary. Kuma yan addinin Hanifiyya da ba sa bautar gumaka su ma suna zuwa Ka’aba su yi ibadarsu.

Ba addini ne ya janyo suka tsani Annabi ba, abin da addinin yazo da shi ne basa so. Banu Umayya sun kashe Imam Hussein suna cikin addinin kakansa saboda ya yi musu abin da suka fi tsana, neman yanci. A gurin Manzon Allah yanci shi ne addini, biyan hakkoki shi ne addini, hana danniya shi ne addini, juyin-juya-hali shi ne addini. Haka Imam Ali ya fahimta, haka Imam Hussein ya aikata.

Sun so su gusar da hasken Allah, amma Allah yaki yarda har sai ya cika haskensa. Shekaru ba adadi suna zagin Imam Ali da danginsa a masallatai amma yanzu ya fi su martaba. Sun kashe yayan Manzon Allah amma yanzu sun fi su nasara.

Aliyu Dahiru Aliyu

15th September, 2018.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post