Idan Ka kashe 'Dan Shi'a YA Zakayi da La'Ilaha-Illallahhun sa Ranar Alkiyama.


.
.
Wannan babban qalubale ne ga duk wani mai da'awar a kashe 'Dan Shi'ah, kawai don an sami bambanci fahinta tsakaninsu, tare da cewa zamanin Annabi ( S.A.W.W ) ko nace lokacin da yake kan gadon rasuwarsa, yayin da yayi umarnin a bashi abin rubutu.
Umar Bn Khaddab ya hana bisa dogaronsa na cewa wai littafin Allah ya ishe su, aka sami masu goya masa baya, yayin da wasu ke ganin abinda Annabi ( S.A.W.W ) yace kawai ayi to ayi.
Duk da wannan sabani na qin bin umarnin Manzo ( S.A.W.W ) bai sa ance jinunsu ya halatta ba.
.
Dalili kuwa shine, sunyi tayayya wajen kadaita Allah da gaskata Manzonsa ( S.A.W.W ), sabanin kawai wajen sallamawa Manzon ne ( S.A.W.W ).
.
.
To kamar haka ne, sanin Kowa ne babu sabani tsakanin Shi'ah da Sunnah wajen kadaita Allah da gaskata Manzonsa ( S.A.W.W ), bambanxin dai kawai shine kamar na magabatan, wato wajen yin biyayyah da bin umarnin Ma'aikin ( S.A.W.W ).
.
Babu Wanda ya isa ya tuhumi 'Dan Shi'ah game da imaninsa ga;
.
ALLAH,
.
MANZONSA ( S.A.W.W ),
.
MALA'IKUNSA ( A.S ),
.
LITTATTAFANSA,
.
KO KUMA MATSAYIN SALLAH.
.
Ban ambaci Zakkah da aikin Hajji bane, domin su aikata su sai Wanda ke da hali.
To, wanne dalili ne yasa kuke halasta ji anan mu?
.
Wata rana Usamatu bin Zaid ya kashe wani mutumin ta yayi kalma Shahada kawai ba tare da ya aikata wani aiki cikin ayyukan muslimci ba, kawai shi Usama ya yiwa mutumin wata fassara ce ta dabam ba tare da yasan haqiqanin abinda me cikin zuciyarsa ba.
.
Ga dai yadda manyan malaman Ahlus-Sunnati na asali suka kawo kamar haka;
.
Manzon Allah ( S.A.W.W ) ya cewa Usama yayin da ya daukaka akan wani mutum da Takobi sai ( mutumin ) yace; " LA'ILAHA-ILLALLAHU ", sai ( shi Usaman ) ya sare shi ya kashe shi.
Sai aka ambatawa Manzon Allah ( S.A.W.W ) hakan, sai ya cewa Usama; " KA KASHE SHI BAYAN YACE LA'ILAHA-ILLALLAHU? YA ZA KAYI DA LA'ILAHA-ILLALLAHUNSA RANAR ALQIYAMA "?
Sai ( Usama ) yace; yaa Manzon Allah, ai ya fadeta ne don neman tsari ( daga rayuwarsa ).
Sai Manzon Allah ( S.A.W.W ) yace; " ME YASA BA KA TSAGA ZUCIYARSA ( ka tantance ) BA "?
Yana fada yana maimaitawa; " YA ZA KAYI DA LA'ILAHA-ILLALLAHUNSA RANAR ALQIYAMA "?
Usama yace; sai da nayi fatan ina ma ban muslimta sai wannan ranar ( saboda muslimci na kankare duk wani abinda mutum ya aikata gabannin muslimci ).
.
- Muslim, J:1, SH:66.
- Sunan Abu Dawud, J:3, SH:44.
- Ibn Majah, J:2, SH:1396.
- Musnad Ahmad, J:5, SH:207.
.
.
To, ka ji fa, Sahabin Manzon Allah ( S
A W.W ) kenan fa Wanda har gobe wannan tuhuma na kansa, ina ga kai Wanda matsayinka bai kai nasa ba?
.
.
Mu dai abinda muka sani shine, jinin mutum musulmi baya halatta sai bisa dayan abubuwa uku;
.
- MUHSININ DA YAYI ZINA ( mace ko namiji ),
.
- WANDA YA KASHE RAI ( da gangan ),
.
- WANDA YAYI RIDDA.
.
Sai kuma daga baya aka fitar da fatawar hukuncin Wanda ya zagi Manzon Allah ( S.A.W.W ) shine kisa.
.
.
TO, KU KUMA A INA KUKA SAMO HUKUNCIN 'DAN SHI'AH MAI SHADAWA DA " LA'ILAHA-ILLALLAHU MUHAMMADUR-RASULULLAH " SHINE KISA ???
.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

.
FREE ZAKZAKY !
FREE ZAKZAKY !!
FREE ZAKZAKY ( H ) !!!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post