IDAN HAR ANNABI(SAW) YA AYYANA SHEKARU 30 A MATSAYIN SHEKARUN KHALIFANCI A BAYANSA; KENAN MU'AWIYA DA KHALIFOFIN DA SU KA BIYO BAYANSA; BA KHALIFOFIN ANNABI(SAW) BA NE? KENAN DUK KHALIFAN DA BAYA CIKIN KHULAFA'UR-RASHIDIN (KHALIFOFI SHIRYAYYU) TO BA SHIRYAYYE BA NE (BATACCE NE) (GAIRU RASHID NE)???
IDAN HAR ANNABI(SAW) YA AYYANA KHALIFOFI 4 A MATSAYIN KHULAFA'UR-RASHIDIN; ME YA SA AKAYI DIMOKRADIYYAR MAGUDI A SAKIFA???
ME YA SA SAHABBAI SU KA TARU A SAKIFA DON ZABEN KHALIFA? KENAN DUK SAHABBAN DA SUKA TARU A SAKIFA JAHILAI NE BASU SAN ANNABI(SAW) YA AYYANA ABUBAKAR A MATSAYIN MAGAJINSA BA???
KENAN ABUBAKAR DA UMAR BA SU SAN ANNABI(SAW) AYYANA SU A MATSAYIN KHALIFOFI BA? TUNDA HAR SU KE MUSAYAR KHALIFANCIN TSAKANIN ABU UBAIDA DA ABUBAKAR; A SAKIFA???
ME YA SA 'YAR ANNABI MUHAMMAD(SAW) [FATIMAH(AS)], HAR TA YI WAFATI BATA YIWA ABUBAKAR MUBAYA'A???
ME YA SA MAFI YAWAN MALAMAN AHLUS-SUNNAH SU KA CE; ANNABI(SAW) BAI FADI WANDA ZAI GAJE SHI BA? KENAN MAFI YAWAN JAMHURIN MALAMAN AHLUS-SUNNAH JAHILAI NE? KO DAI BA SU YARDA DA INGANCIN HADISAN KHALIFANCIN ABUBAKAR BA NE???
IDAN UMAR YA SAN ANNABI(SAW) YA AYYANA USMAN; ME ZAI SA SAI TA HANYAR SHURA ZA'A ZABI USMAN? KENAN UMAR DA YAN KWAMITIN SHURAR SUN JAHILCI AYYANAWAR ANNABI(SAW)???
ME YA SA UMMUL-MU'UMIN AISHA TA HARZUKA SAHABBAI AKAN AYIWA KHALIFA USMAN TAWAYE? KENAN UMMUL-MU'UMININ AISHA BATA SAN ANNABI(SAW) YA AYYANA USMAN A MATSAYIN KHALIFA BA? INA MAKOMAR SAHABBAI DA TABI'AN DA SU KA KASHE USMAN???
ME YA SA UMMUL-MU'UMININ AISHA, MU'AWIYA... SUKA YIWA IMAM ALI(AS) TAWAYE? MENENE MAKOMAR WANDA YA YAKI DAYA DAGA CIKIN KHULAFA'UR-RASHIDIN???
INA MAKOMAR HADISIN KHALIFOFI 12 A BAYAN ANNABI(SAW)? KO BAI INGANTA BA NE? KO DAI AHLUS-SUNNAH KUNA SO KUCE; ANNABI(SAW) YA YI MAGANAR DA AKASINTA YA FARU???
DUK DUNIYA AKWAI WATA JAMA'A MAI KHALIFOFI 12; BANDA SHI'A IMAMIYYA???
YA ALLAH KA BARMU DA IMAMAN SHIA 12; DUNIYA DA LAHIRA! KA KARBI AYUKANMU!! KA BIYA MANA BUKATUNMU; ALBARKACINSU(AS)!!!
➖➖➖➖➖➖➖➖
Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmail.com
🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹
Tags:
Taskar ilimi