IDAN HAR AKWAI WATA AYAR QUR'ANI DA TA CE AYI KOYI DA SAHABBAI, SHIN IMAM ALI(AS) BA SAHABI BA NE? SAYYIDAH FATIMAH BA SAHABIYA BA CE? IMAM HASAN(AS), HUSAIN(AS)... BA SAHABBAI BA NE?E KENEN KOYI DA AHLUL-BAYT(AS) NE YA FI, SABODA AHLUL-BAYT(AS) SUMA SAHABBAI NE, DORIYA AKAN FIFIKONSU NA KASANCEWAR SU ZURIYAR ANNABI MUHAMMAD(SAW) DA KUMA AYOYI DA HADISAN DA KE ALAMTA WAJABCIN RIKO DA SU.
BABU WATA AYAR QUR'ANI DA TA ALAMTA ALLAH YA CE; MU YI KOYI DA DUKKAN SAHABBAI KACOKAF. IDAN HAR ALLAH ZAI CE MU KOYI DA DUKKAN SAHABBAI KACOKAF; KENAN A CIKIN SAHABBAI BA WANDA YA TABA SABAWA ALLAH? KENAN SAHABBAI RANKATAKAF MA'ASUMAI NE? IDAN AKWAI SAHABIN DA YA TABA SABAWA ALLAH; KENAN ALLAH YA CE MUYI KO DA WANI A CIKIN SABA MASA???
BABU WANI INGANTACCEN HADISI DA ANNABI MUHAMMAD(SAW) YA CE; MU BI TAFARKIN DUKKAN SAHABBAI KACOKAF, IDAN HAR ANNABI(SAW) ZAI CE MU YI KOYI DA SAHABBAI RANKATAKAF; ME YA SA ZAI CE CIKIN SAHABBAI AKWAI FI'ATUL-BAGIYA (AZZALUMAI)? ME YA SA ZAI CE CIKIN SAHABBANSA AKWAI 'YAN WUTAR JAHANNAMAH? KENAN ANNABI(SAW) YANA UMARTAR MU DA MUYI KOYI DA 'YAN WUTA? INA KOYI DA AIKIN 'YAN WUTA ZAI KAI MU???
SAHABBAN DA KANSU BA SU CE A YI KOYI DA SU BA. KO AKWAI INDA WANI SAHABI DA BAYA CIKIN AHLUL-BAYT(AS) DA YA CE A YI KOYI DA DUKKAN AIKINSA RANKATAKAF???
IDAN KOYI DA SAHABBAI WAJIBI NE; KENAN WAJIBI NE MUSULMI SU KE KASHE JUNAN SU, KAMAR YANDA SAHABBAI SU KA YI A YAKIN JAMAL, SIFFIN, NAHARAWAN...???
WANI MALAMIN FIQHU NE YA SAKA AIKIN SAHABBAI KACOKAF CIKIN MASDARORIN SHARI'A? IDAN AIKIN SAHABBAI RANKATAKAF YA NA CIKIN MASDARORIN SHARIA; TO YA ZAMU YI DA INDA SAHABBAI SU KE DA SABANI? KO SAHABBAI BA SU TABA SAMUN BAMBANCIN FAHIMTA A TSAKANINSU BA? KENAN DOLE AKWAI SAHABIN DA YA KE AKAN DAIDAI WANI SAHABIN KUMA AKAN KUSKURE? TA YA KUSKURE ZAI ZAMA MASDARIN SHARIA???
Ahlus-sunnah kan ce wai Allah wajabta koyi da Sahabbai da nassin wasu Ayoyin Qur'ani, kamar:
Fadin Allah:
وَالسّابِقونَ الأَوَّلونَ مِنَ المُهاجِرينَ وَالأَنصارِ وَالَّذينَ اتَّبَعوهُم بِإِحسانٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنهُم وَرَضوا عَنهُ وَأَعَدَّ لَهُم جَنّاتٍ تَجري تَحتَهَا الأَنهارُ خالِدينَ فيها أَبَدًا ۚ ذٰلِكَ الفَوزُ العَظيمُ
(Quran - 9 : 100).
Mahallush-Shahid din da Ahlus-sunnah ke kafa hujja da shi akan wajabta koyi da Sahabbai a ayar:
وَالَّذينَ اتَّبَعوهُم بِإِحسانٍ
BA DUKAN SAHABBAI NE َالسّابِقونَ الأَوَّلونَ, DON HAKA AYAR BA TA WAJABTA KOYI DA DUKAN SAHABBAI.
IMAM ALI(AS), SAYYIDAH FATIMAH(AS)... SU NA CIKIN َالسّابِقونَ الأَوَّلون, KENAN AYAR TA NA WAJABTA KOYI DA SU, IDAN HAR AYAR TA NA ALAMTA WAJABCIN KOYI DA السّابِقونَ الأَوَّلون.
Fadin Allah:
ﻭَﻣَﻦْ ﻳُﺸَﺎﻗِﻖِ ﺍﻟﺮَّﺳُﻮﻝَ ﻣِﻦْ ﺑَﻌْﺪِ ﻣَﺎ ﺗَﺒَﻴَّﻦَ ﻟَﻪُ ﺍﻟْﻬُﺪَﻯ ﻭَﻳَﺘَّﺒِﻊْ ﻏَﻴْﺮَ ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ ﻧُﻮَﻟِّﻪِ ﻣَﺎ ﺗَﻮَﻟَّﻰ ﻭَﻧُﺼْﻠِﻪِ ﺟَﻬَﻨَّﻢَ ﻭَﺳَﺎﺀَﺕْ ﻣَﺼِﻴﺮًﺍ. (ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : 115).
"Mahallush-Shahid din da Ahlus-sunnah ke kafa hujja da shi akan wajabta koyi da Sahabbai a ayar:
ﻭَﻳَﺘَّﺒِﻊْ ﻏَﻴْﺮَ ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦ
Ayar ta fara gargadi ne akan sabawa umarnin Annabi Muhammad(saw) (ﻭَﻣَﻦْ ﻳُﺸَﺎﻗِﻖِ ﺍﻟﺮَّﺳُﻮﻝَ), kenan Allah ya yi umarni akan a bi Annabi(saw) kafin Sahabbai? Kenan idan Sahabi ya sabawa Annabi(saw) to Annabi(saw) zamu bi; ba Sahabi ba? Duk Sahabin da ya Sabawa Annabi(saw); to dole ne a saba masa.
Tarihi ya tabbatar mana da cewa; Sahabbai da yawa sun sabawa Allah da Annabi(saw), kuma tunda Sahabbai ba Ma'sumai ba ne; zai yiwu suyi kuskure.
Bari mu bada 'yan misalai kadan a guraren da Sahabbai suka sabawa Annabi(saw) kamar yanda ya zo a Qur'ani da ingantattun hadisai:
Sahabbai sun saba Annabi(saw) a ranar Sulhul-hudaibiyya. Annabi(saw) ya ce ayi Sulhu da kafiran Quraishawa, ayi aski a koma Madina, wasu Sahabbai suka ce; sam ba su yarda ba, wani sahabin ma cewa yayi; al'amarin Sulhul-Hudaibiyya ya sa masa shakku akan annabtar Annabi Muhammad(saw):
Sahabbai sun sabawa Annabi(saw) a ranar yakin Uhudu, Hunain... Saboda sabawa Annabi(saw) da Sahabbai suka yi a wadancan yakokin ya jawo kafirai suka ci galaba akan Sahabbai, sai da ma wasu Sahabbai suka ranta a na kare daga fagen daga.
Ummul-muminin Aisha ta jahoranci Sahabbai wajen yiwa Annabi(saw) dure a rashin lafiyar da yayi shahada a cikinta; duk da cewa Annabi(saw) ya hana su kuma ya gargadesu da kar suyi masa duren. (kamar yanda Bukhari, Muslim... suka ruwaito).
Ummul-muminin Hafsah 'yar Umar dan Khattab tayi ja-in-ja da Annabi(saw) har takai Annabi(saw) ya saketa, kuma babanta Umar ya tabbatar mana da cewa; wallahi Annabi(saw) bai sonta, ba don Umar din ba da Annabi(saw) bai mayar da aurenta ba. (Kamar yanda Muslim... suka ruwaito).
Idan Allah ya ce ayi koyi da Sahabbai rankatakaf; kenan sai muyi ko da Ummul-muminin Hafsah?
Sahabbai sun Sabawa Annabi(saw) a ranar Alhamis din karshe a rayuwarsa(saw). Annabi(saw) ya ce a kawo masa takarda ya ruba mana abinda ba zamu halaka a bayansa, wani Sahabi ya ce; "Annabi(saw) ya zautu, bai san me ya ke fada ba, littafin Allah ya ishemu". Wannan ne ya sa Annabi(saw) kori Sahabban da ke gurin, kuma wasu daga cikinsu basu kara dawo wajen Annabi(saw) ba sai bayan taron Sakifa.
Sahabbai sun sabawa Annabi(saw) akan al-amarin Ghadir. Annabi(saw) ya ce a jibinci Imam Ali(as), sai Sahabbai suka yi dimukradiyyar magudi a Sakifa.
Idan ma mun kaddara hadisin Ghadir yana nufin a so Imam Ali(as) ne, to Sahabbai sun sabawa Annabi(saw) ta hanyar yakar Imam Ali(as) a Jamal, Siffin, Naharawan...
Misalai akan yanda wasu Sahabbai suka sabawa Annabi(saw) yana da yawan gaske, mai bukatar cikakken bayani zai iya komawa zuwaga littattafan Tafsiri, Hadisi, Tarihi...
AIKIN DUKKAN SAHABBAI KACOKAF BAYA CIKIN MASDARORIN SHARIA. QUR'ANI DA INGANTATTUN HADISAI SUNE MASDARORIN SHARIA.
Don Allah(swt) ya tabbatar mana da cewa Qur'ani da ingantattun hadisai ne masdarorin Sharia; sai Allah(swt) yake cewa:
ﻭَﻣَﺎ ﺍﺧْﺘَﻠَﻔْﺘُﻢْ ﻓِﻴﻪِ ﻣِﻦ ﺷَﻲْﺀٍ ﻓَﺤُﻜْﻤُﻪُ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ.
"Duk abinda ku ke da sabani akansa, to hukuncinsa yana ga Allah(swt) (Qur'ani)".
(ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ : 10).
Wannan ayar tana nuna mana cewa; Qur'ani shine masdarin Sharia na farko.
A wata ayar Allah(swt) yana cewa:
...ﻓَﺈِﻥ ﺗَﻨَﺎﺯَﻋْﺘُﻢْ ﻓِﻲ ﺷَﻲْﺀٍ ﻓَﺮُﺩُّﻭﻩُ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠّﻪِ ﻭَﺍﻟﺮَّﺳُﻮﻝِ ﺇِﻥ ﻛُﻨﺘُﻢْ ﺗُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ ﺑِﺎﻟﻠّﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻵﺧِﺮِ ﺫَﻟِﻚَ ﺧَﻴْﺮٌ ﻭَﺃَﺣْﺴَﻦُ ﺗَﺄْﻭِﻳﻼً.
"Idan kuna da sabani akan wani abu; to ku koma zuwaga Allah(swt) (Qur'ani) da Manzo(saw) (inagantattun hadisai), matukar kun yi imani da Allah(swt) da ranar Lahira. (komawa zuwaga Qur'ani da ingantattun Hadisai) shine mafi alkhairi kuma mafi kyaun tawili".
(ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : 59).
Imam Ali(as) ya tabbatar da aikin dukkan Sahabbai kacokaf bai cikin masdarin Sharia, wannan ya faru ne a lokacin da Khalifa Umar Ibn Khattab ya kafa 'yan kwamitin Shura, da suka kafawa Imam Ali(as) sharadi akan cewa; idan yana so su zabe shi khalifan da zai gaji Umar; lalle zai yi khalifanci irin na Khalifa Abubakar da Umar, sai Imam Ali(as) ya ce; zai dai yi khalfanci karkashin koyarwar ayoyin Qur'ani da ingantattun Hadisai. Idan har aikin khalifa Abubakar da Umar ba lalle ya zama; masdarin Sharia ba; to wane Sahabi ne aikinsa zai zama masdarin Sharia?:
ﻭﻟﺬﻟﻚ ﻧﺠﺪ ﺃﻥّ ﻋﻠﻴّﺎً(ع) ﺣﻴﻨﻤﺎ ﻋﺮﺿﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺨﻼﻓﺔ ﻓﻲ ﻗﻀﻴﺔ ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺴﺘّﺔ ﺑﺸﺮﻁ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺑﻜﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳُﻨّﺔ ﺍﻟﻨﺒﻲّ ﻭﺳﻴﺮﺓ ﺍﻟﺸﻴﺨﻴﻦ، ﺭﻓﺾ ﻋﻠﻲّ(ع) ﺫﻟﻚ ﻭﻟﻢ ﻳﻘﺒﻞ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺇﻻّ ﺑﻜﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳُﻨّﺔ ﻧﺒﻴّﻪ، ﻭﻟﻢ ﻳﺮﺽَ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺑﺴﻴﺮﺓ ﺍﻟﺸﻴﺨﻴﻦ. (ﺷﺮﺡ ﻧﻬﺞ ﺍﻟﺒﻼﻏﺔ : 1 : 188 ﻗﺼّﺔ ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ. ﺍﻟﻤﺤﺼﻮﻝ ﻟﻠﺮﺍﺯﻱ : 6 : 86...).
IMAM ALI(AS) NE "MUMININ" KUMA TAFARKINSA NE ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ DON HAKA SABANIN HANYAR IMAM ALI(AS) ITA CE ﻏَﻴْﺮَ ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ. DALILIN DA YA TABBATAR DA HAKAN KUWA ITA CE AYAR WILAYA:
Ayar Wilayah (آية الولاية)(Ayar Shugabanci):
ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻭَﻟِﻴُّﻜُﻢُ ﺍﻟﻠّﻪُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍْ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳُﻘِﻴﻤُﻮﻥَ ﺍﻟﺼَّﻼَﺓَ ﻭَﻳُﺆْﺗُﻮﻥَ ﺍﻟﺰَّﻛَﺎﺓَ ﻭَﻫُﻢْ ﺭَﺍﻛِﻌُﻮﻥَ. ﻭَﻣَﻦ ﻳَﺘَﻮَﻝَّ ﺍﻟﻠّﻪَ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟَﻪُ ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍْ ﻓَﺈِﻥَّ ﺣِﺰْﺏَ ﺍﻟﻠّﻪِ ﻫُﻢُ ﺍﻟْﻐَﺎﻟِﺒُﻮﻥَ. (ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ: ﺁﻳﺔ 55)
"Tabbas Allah(swt) ne majibincin lamarinku, Sannan Manzonsa(saw) (shine shugabanku), (a bayan Annabi(saw) wadanda suke shuwagabanninku sune) wadanda suka yi Imani (Muminin), suna tsayar da Sallah, suna bada sadaka a yayinda suke ruku'u. Duk wanda ya jibinci Allah, Manzonsa(saw) da wadanda da suka yi imani (Muminin); (to yana cikin rundunar Allah) kuma rundunar Allah sune masu cin nasara (akan duk abinda suka dosa)"(Q:5:55).
Wannan ayar ta wilaya an saukar da ita ne a ranar 24, ga watan Zul-Hijja, bayan Annabi Muhammad(saw) yayi Mubahala da Kiristocin Najran, lokacin da ya zabi Imam Ali(as), Sayyidah Fatimah(as), Imam Hasan(as) da Imam Husain(as) a matsayin wadanda suka fi kowa dajara a wajen Allah da Annabi(saw) (Q;3:61), kuma Annabi(saw) ya tabbatar da sune Ahlul-bayt(as) da Hadisul-kisa'i, Sannan Mala'ika Jibril(as) ya zo da Ayatut Tat'hir (Q:33:33):
6587 - ﺣﺪﺛﻨﺎ : ﺃﺑﻮ ﺳﻌﻴﺪ ﺍﻷﺷﺞ، ﺛﻨﺎ: ﺍﻟﻔﻀﻞ ﺑﻦ ﺩﻛﻴﻦ ﺃﺑﻮ ﻧﻌﻴﻢ ﺍﻷﺣﻮﻝ، ﺛﻨﺎ: ﻣﻮﺳﻰ ﺑﻦ ﻗﻴﺲ ﺍﻟﺤﻀﺮﻣﻲ، ﻋﻦ ﺳﻠﻤﺔ ﺑﻦ ﻛﻬﻴﻞ، ﻗﺎﻝ: ﺗﺼﺪﻕ ﻋﻠﻲ ﺑﺨﺎﺗﻤﻪ ﻭﻫﻮ ﺭﺍﻛﻊ ﻓﻨﺰﻟﺖ: ﺇﻧﻤﺎ ﻭﻟﻴﻜﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻘﻴﻤﻮﻥ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﻳﺆﺗﻮﻥ ﺍﻟﺰﻛﺎﺓ ﻭﻫﻢ ﺭﺍﻛﻌﻮﻥ.
(ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺇﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺣﺎﺗﻢ - ﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ: ﺇﻧﻤﺎ ﻭﻟﻴﻜﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ).
Wannan ayar ta wilaya an saukar da ita ne a lokacin da Imam Ali(as) yayi sadaka da zobinsa a Masallacin Annabi(saw). Malaman Tafsiri, Hadisi da As-babun Nuzul... sun tambatar da cewa wannan ayar ta wilaya an saukar da ita ne akan al'amarin khalifancin Imam Ali(as):
ﺫﻛﺮ ﺍﻟﻤﻔﺴّﺮﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻳﺮﺑﻮ ﻣﻦ ﺃﺭﺑﻌﻴﻦ ﻛﺘﺎﺑﺎً ﻧﺰﻭﻝ ﻫﺬﻩ ﺍﻵﻳﺔ ﻓﻲ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ(ﻉ) ﺑﻌﺪ ﻗﺼﺔ ﺗﺼﺪّﻗﻪ ﺑﺨﺎﺗﻤﻪ ﻭﻫﻮ ﺭﺍﻛﻊ ﻓﻲ ﺻﻼﺗﻪ ﻭﻣﻤﻦ ﺫﻛﺮ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﻋﻠﻤﺎﺀ ﺟﻤﻬﻮﺭ؛ ﻓﺨﺮ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻟﺮﺍﺯﻱ (ﺍﻟﻤﺘﻮﻓﻰ 406 ﻫـ).ﺟﺎﺭ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺰﻣﺨﺸﺮﻱّ (ﺍﻟﻤﺘﻮﻓﻰ 825 ﻫـ ) ﻗﺎﻝ ﻓﻲ ﺗﻔﺴﻴﺮ ﻫﺬﻩ ﺍﻵﻳﺔ، ﻭﺇﻧﻬﺎ ﻧﺰﻟﺖ ﻓﻲ ﻋﻠﻰّ (ﻛﺮﻡ ﺍﻟﻠَّﻪ ﻭﺟﻬﻪ)(ﺍﻟﻜﺸﺎﻑ ﻋﻦ ﺣﻘﺎﺋﻖ ﻏﻮﺍﻣﺾﺍﻟﺘﻨﺰﻳﻞ، ﺟﺎﺭ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺰﻣﺨﺸﺮﻱّ، ﺝ 1، ﺹ 649).
Sahabi Abu Zar(r) ya ce wata rana muna tare da Annabi(saw) a masallaci sai ga wani mai bara ya shigo masallacin, ya nemi sadaka bai samu ba; sai ya daga hannunsa yayi addu'a yace; "ya Allah ka shaida na zo masallacin Annabi(saw) na yi bara ba wanda ya bani". Sai Imam Ali(as) yayi masa ishara da hannunsa ya cire zoben sa. Bayan da mai baran ya cire zoben, lokacin Annabi(saw) yana gurin, sai Annabi(saw) ya daga hannunsa yayi addu'a, kamar haka; "Ya Allah! Annabi Musa(as) ya roki ka karfafeshi da dan uwansa Harun(as), ka karba addu'arsa.... Ya Allah! Ni Annabinka Muhammad(saw) ina rokonka ka karfafeni da Ali(as) ka sanyashi ya zama shugaba (a bayana)". Rufe bakin Annabi(saw) ke da wuya, sai ga mala'ika Jibril(as) da wannan ayar wilaya. Dalilin haka ne Annabi(saw) ya ce; "Ali(as) a wajena tamkar Harun(as) ne a wajen Musa(as).
Ga nassin hadisin:
ﺭﻭﻱ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺫﺭ(ر) ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ ﺻﻠﻴﺖ ﻣﻊ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠَّﻪ(ﺹ) ﻳﻮﻣﺎً ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻈﻬﺮ، ﻓﺴﺄﻝ ﺳﺎﺋﻞ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻓﻠﻢ ﻳﻌﻄﻪ ﺃﺣﺪ، ﻓﺮﻓﻊ ﺍﻟﺴﺎﺋﻞ ﻳﺪﻩ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻳﻘﻮﻝ: ﺍﻟﻠّﻬﻢ ﺍﺷﻬﺪ ﺃﻧﻲ ﺳﺄﻟﺖ ﻓﻲ ﻣﺴﺠﺪ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ(ﺹ) ﻓﻤﺎ ﺃﻋﻄﺎﻧﻲ ﺃﺣﺪ ﺷﻴﺌﺎ، ﻭﻋﻠﻲ ﻛﺎﻥ ﺭﺍﻛﻌﺎً، ﻓﺄﻭﻣﺄ ﺇﻟﻴﻪ ﺑﺨﻨﺼﺮﻩ ﺍﻟﻴﻤﻨﻰ ﻭﻛﺎﻥ ﻓﻴﻬﺎ ﺧﺎﺗﻢ، ﻓﺄﻗﺒﻞ ﺍﻟﺴﺎﺋﻞ ﺣﺘﻰ ﺃﺧﺬ ﺍﻟﺨﺎﺗﻢ ﺑﻤﺮﺃﻯ ﺍﻟﻨﺒﻲ(ﺹ) ﻓﻘﺎﻝ: "ﺍﻟﻠّﻬﻢ ﺇﻥ ﺃﺧﻲ ﻣﻮﺳﻰ ﺳﺆﻟﻚ، ﻓﻘﺎﻝ: ﺭَﺏِّ ﺍﺷْﺮَﺡْ ﻟِﻲ ﺻَﺪْﺭِﻱ ﺇﻟﻰ ﻗﻮﻟﻪ ﻭَﺃَﺷْﺮِﻛْﻪُ ﻓِﻲ ﺃَﻣْﺮِﻱ [ﻃﻪ : 32-25] ﻓﺄﻧﺰﻟﺖ ﻗﺮﺁﻧﺎ ﻧﺎﻃﻘﺎ؛ ﺳَﻨَﺸُﺪُّ ﻋَﻀُﺪَﻙَ ﺑِﺄَﺧِﻴﻚَ ﻭَ ﻧَﺠْﻌَﻞُ ﻟَﻜُﻤﺎ ﺳُﻠْﻄﺎﻧﺎً [ﺍﻟﻘﺼﺺ : 35] ﺍﻟﻠّﻬﻢ ﻭﺃﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻧﺒﻴﻚ ﻭﺻﻔﻴﻚ ﻓﺎﺷﺮﺡ ﻟﻲ ﺻﺪﺭﻱ ﻭﻳﺴﺮ ﻟﻲ ﺃﻣﺮﻱ ﻭﺍﺟﻌﻞ ﻟﻲ ﻭﺯﻳﺮﺍ ﻣﻦ ﺃﻫﻠﻲ ﻋﻠﻴﺎ ﺃﺷﺪﺩ ﺑﻪ ﻇﻬﺮﻱ. ﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮﺫﺭ ﻓﻮﺍﻟﻠَّﻪ ﻣﺎ ﺃﺗﻢ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠَّﻪ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻜﻠﻤﺔ ﺣﺘﻰ ﻧﺰﻝ ﺟﺒﺮﻳﻞ ﻓﻘﺎﻝ ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻗﺮﺀ: ﺇِﻧَّﻤﺎ ﻭَﻟِﻴُّﻜُﻢُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪ... ﺇﻟﻰ ﺁﺧﺮﻫﺎ
(ﻣﻔﺎﺗﻴﺢ ﺍﻟﻐﻴﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ، ﺍﻟﻔﺨﺮ ﺍﻟﺮﺍﺯﻱ، ﺝ 21، : ﺹ 382. ﺍﻟﺴﻴﻮﻃﻲ - ﺍﻟﺪﺭ ﺍﻟﻤﻨﺜﻮﺭ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻔﺴﻴﺮ ﺑﺎﻟﻤﺄﺛﻮﺭ - ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ: 55 ﺍﻟﺠﺰﺀ : 3 - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : 104 / 105.ﺃﺑﻲ ﻧﻌﻴﻢ ﺍﻹﺻﺒﻬﺎﻧﻲ - ﻣﻌﺮﻓﺔ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ - ﺣﺮﻑ ﺍﻷﻟﻒ. ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ - ﻣﻌﺮﻓﺔ ﻋﻠﻮﻡ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ - ﺫﻛﺮ ﺍﻟﻨﻮﻉ ﺍﻟﺨﺎﻣﺲ ﻭﺍﻟﻌﺸﺮﻳﻦ ﻣﻦ ﻋﻠﻢ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ. ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﺒﺎﻗﺮ - ﺣﻠﻴﺔ ﺍﻷﻭﻟﻴﺎﺀ - ﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ﺇﻧﻤﺎ ﻭﻟﻴﻜﻢ ﺍﻟﻠﻪ. ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﺒﻴﻀﺎﻭﻱ - ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ - ﺍﻵﻳﺔ : 55. ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﺮﻃﺒﻲ - ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ - ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ - ﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ: ﺇﻧﻤﺎ ﻭﻟﻴﻜﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ - ﺍﻟﺠﺰﺀ : 6 - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : 161...).
Manyan malaman Ahlus-Sunnah sun ruwaito hadisai mutawaturai da suka nuna wannan ayar ta sauka ne saboda Imam Ali(as) yayi sadaka da zobinsa a lokacin da yake ruku'u, kuma Annabi(as) ya tabbatar da cewa wannan aikin kadai ya wajabtawa Imam Ali(as) Al-Jannah.
Ga nassin hadisin:
ﺃﺑﻮ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻜﻨﺠﻲ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ (ﺍﻟﻤﺘﻮﻓﻰ 856: ﻫـ) : ﻓﻘﺪ ﺭَﻭﻯ ﻋﻦ ﺃﻧﺲ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﺃﻥّ ﺳﺎﺋﻼً ﺃﺗﻰ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻭﻫﻮ ﻳﻘﻮﻝ: ﻣﻦ ﻳﻘﺮﺽ ﺍﻟﻤﻠﻲ ﺍﻟﻮﻓﻲ؟ ﻭﻋﻠﻲ(ﻉ) ﺭﺍﻛﻊ ﻳﻘﻮﻝ ﺑﻴﺪﻩ ﺧﻠﻔﻪ ﻟﻠﺴﺎﺋﻞ ﺃﻥ ﺍﺧﻠﻊ ﺍﻟﺨﺎﺗﻢ ﻣﻦ ﻳﺪﻱ، ﻓﻘﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ( ﺹ ) : ﻳﺎ ﻋﻤﺮ! ﻭﺟﺒﺖ؛ ﻗﺎﻝ ﺑﺄﺑﻲ ﺃﻧﺖ ﻭﺃﻣﻲ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻣﺎ ﻭﺟﺒﺖ؟ ﻗﺎﻝ ﻭﺟﺒﺖ ﻟﻪ ﺍﻟﺠﻨﺔ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﺧﻠﻌﻪ ﻣﻦ ﻳﺪﻩ ﺣﺘﻰ ﺧﻠﻌﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﻛﻞ ﺫﻧﺐ، ﻭﻣﻦ ﻛﻞ ﺧﻄﻴﺆﺓ، ﻗﺎﻝ ﻓﻤﺎ ﺧﺮﺝ ﺃﺣﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﺣﺘﻰ ﻧﺰﻝ ﺟﺒﺮﺋﻴﻞ(ﻉ) ﺑﻘﻮﻟﻪ ﻋﺰ ﻭ ﺟﻞ ﴿ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻭَﻟِﻴُّﻜُﻢُ ﺍﻟﻠّﻪُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍْ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳُﻘِﻴﻤُﻮﻥَ ﺍﻟﺼَّﻼَﺓَ ﻭَﻳُﺆْﺗُﻮﻥَ ﺍﻟﺰَّﻛَﺎﺓَ ﻭَﻫُﻢْ ﺭﺍﻛﻌﻮﻥ.
( ﻛﻔﺎﻳﺔ ﺍﻟﻄﺎﻟﺐ، ﺍﻟﻜﻨﺠﻲ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ، ﺍﻟﺒﺎﺏ 16، ﺹ 228. ﺍﺑﻦ ﻛﺜﻴﺮ - ﺍﻟﺒﺪﺍﻳﺔ ﻭﺍﻟﻨﻬﺎﻳﺔ - ﺳﻨﺔ ﺃﺭﺑﻌﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻬﺠﺮﺓ ﺍﻟﻨﺒﻮﻳﺔ
ﺑﺎﺏ ﺫﻛﺮ ﺷﻲﺀ ﻣﻦ ﻓﻀﺎﺋﻞ ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ (ﺭ)
ﺣﺪﻳﺚ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ ﺑﺎﻟﺨﺎﺗﻢ ﻭﻫﻮ ﺭﺍﻛﻊ
ﺍﻟﺠﺰﺀ : 11 - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : 93. ﺍﺑﻦ ﻛﺜﻴﺮ - ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ - ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ - ﺗﻔﺴﻴﺮ ﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﻣَﻦ ﻳَﺮْﺗَﺪَّ ﻣِﻨﻜُﻢْ ﻋَﻦ ﺩِﻳﻨِﻪِ ﻓَﺴَﻮْﻑَ ﻳَﺄْﺗِﻲ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺑِﻘَﻮْﻡٍ ﻳُﺤِﺒُّﻬُﻢْ ﻭَﻳُﺤِﺒُّﻮﻧَﻪُ (ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ : 54) ﺍﻟﺠﺰﺀ : 3 - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : 138. ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ - ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ = ﺟﺎﻣﻊ ﺍﻟﺒﻴﺎﻥ ﻋﻦ ﺗﺄﻭﻳﻞ ﺁﻱ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ. ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻓﻲ ﺗﺄﻭﻳﻞ ﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻭَﻟِﻴُّﻜُﻢُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳُﻘِﻴﻤُﻮﻥَ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَﻳُﺆْﺗُﻮﻥَ ﺍﻟﺰَّﻛَﺎﺓَ ﻭَﻫُﻢْ ﺭَﺍﻛِﻌُﻮﻥَ (ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ : 55). ﺍﻟﺠﺰﺀ : 8 - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : 531...).
Kadan daga cikin malaman Ahlus-Sunnah da suka ambaci cewa ayar wilaya an saukar da ita akan al'amarin Imam Ali(as):
1. Imam Fakhrud-Din Razi, a Tafsir Kabir, j; III, s; 431.
2. Imam Abu Ishaq Tha'labi, a Kashful Bayan.
3. Jarullah Zamakhshari, a Tafsir Kashshaf, j; I, s; 422.
4. Tabari, a Tafsir, J; VI, S; 186.
5. Abul Hasan Rammani, a Tafsir,
6. Ibn Hawazin Nishapuri, a Tafsir.
7. Qartabi, a Tafsir, j; VI, s; 221.
8. Nasafi Hafiz, a Tafsir, s; 496.
9. Khazin Baghdadi, a Tafsir.
10. Fazil Nishapuri, a Gharibul-Qur'an, j; I, s; 461.
11. Wahidi, a Asbabun-Nuzul, s; 148.
12. Hafiz Abubakar Jassas, a Tafsir Ahkamul Qur'an, s; 542;
13. Hafiz Abu Bakr Shirazi, a Fima Nazala Minal Qur'an Fi Amirul Mu'minin.
14. Qazwini, a Tafsir Kabir.
15. Qazi Baidhawi, a Anwarut-Tanzil, j; I, s; 345.
16. Suyuti, a Durrul-Mansur, j; II, s; 239.
17. Qazi Shukani, a Tafsir Fathul-Qadir.
18. Alusi, a Tafsir, j; II, s; 329.
19. Hafiz Ibn Abi Shaiba Kufi, a Tafsir.
20. Abul Baraka, a Tafsir, j; I, s; 496.
21. Hafiz Baghawi, a Ma'alimut-Tanzil.
22. Nisa'i, a Sunan.
23. Muhammad Bin Talha Shafi'i, a Matalibus-Su'ul, s; 31.
24. Ibn Abil Hadid, a Sharh Nahjul-Balagha, j; III, s; 375.
25. Khazin Ala'u'd-Din Baghdadi, a Tafsir, j; I, s; 496.
26. Sulayman Hanafi, a Yanabiul-Mawadda, s; 212.
27. Hafiz Abu Bakr Baihaqi, a Kitab Musannaf.
29. Razin Abdari, a Jam' Bainus-Siha Sitta.
30. Ibn Asakir Damishqi, a Ta'rikh Dimashq.
31. Sibt Ibn Jauzi, a Tadhkira, s; 9,
32. Qazi Azuda'iji, a Mawaqif, s; 276.
33. Seyyed Sharif Jurjani, a Sharh Mawaqif.
34. Ibn Sabbagh Maliki, a Fusulul-Muhimma, s; 123.
35. Hafiz Abu Sa'd Sam'ani, a Faza'ili's-Sahaba.
36. Abu Ja'far Askafi, a Nagzil-Uthmaniyya.
37. Tibrani, a Ausat.
38. Ibn Maghazili Faqih Shafi'i, a Manaqib.
39. Muhammad bin Yusuf Ganji Shafi'i, a Kifayatu't-Talib.
40. Ali Qushachi, a Sharh Tajrid.
41. Shablanji, a Nuru'l-Absar, s; 77.
41. Muhibud-Din Tabari, a Riyazun-Nuzra, j; II, s; 247. Da sauransu.
Wadannan hadisan da suka tabbatar da ayar wilaya ta sauka akan yabon Imam Ali(as); mutawaturai ne, sahabbai da dama sun ruwaito su. Kadan daga cikinsu; Abdullah Ibn Abbas, Abu Dharr Ghifari, Jabir Ibn Abdullah Ansari, Ammar, Abu Rafi', Sadi, Mujahid Hasan Basri, A'mash, Atba Bin Hakim, Ghalib Ibn Abdullah, Qais Bin Rabi'a, Abaya Bin Rab'i, Abdullah Bin Salam, da sauransu, dukkansu sun riwaito wannan ayar ta wilaya ta sauka ne akan yabon Imam Ali(as).
➖➖➖➖➖➖➖➖
Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmail.com
🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com