* MA'ASUMIYA NIGERIAN NEWS UPDATES
Idan muka ce (IMFAQI), muna nufin abinda mutum zai cire ya bayar dashi don yiwa addinin Muslimci da musulmai hidima, kudi ne ko kuma kaddara.
Shi addin Allah ba ya gudana ko kuma cigaba yadda ya kamata dole sai an sanya dukiya cikinsa. Shi yasa aka saukar da ayoyi masu yawa da hadisan Ma'aiki (S.A.W.W) masu yin umarni kan yinsa.
Matsalar da ake samu ce, za muga da yawa daga masu kiran kansu 'yan qungiya na addini, sukan nemi kudi da sunan yiwa muslinci hidima, amma idan aka tara misalin #100,000 sai kaga abinda zai tafi ta hanyar dalilin tattara wadannan kudade bai wuce #60,000 ba, #40,000 ta tafi qarqashin qarya da gaskiya, wato masu jagorantar al'amarin sun cinye a tsakaninsu.
Wannan ya sanya da yawa suna fassara cewa abubuwa da ake tarawa da sunan yin wani aiki ba a gudanar shi yadda ya kamata. Hakan kuwa yayi sanadin wasu sukan qi bayarwa saboda zargin hakan, yin wannan zargi kuwa ba daidai bane (a harka), kuma ba hujja ce karbabbiya ba.
Wata rana Manzon Allah (S.A.W.W) yayi magana kan bayar da zakkah ga dangi, masu roqo, maqwabta da miskinai, sai wani mutum yace, yaa Mà'aikin Allah, kana ganin ya wadatar min idan na bayar da zakkah ga dan saqonka, na kubuta daga gare ta zuwa ga Allah da Manzonsa (S.A.W.W) ?
Sai Manzon Allah (S.A.W.W) yace;
" EH, IDAN KA BAYAR DA ITA GA 'DAN SAQONA HAQIQA KA KUBUTA DAGA GARE TA, KANA DA LADANTA, LAIFINTA YANA KAN WANDA YA CANZA TA (zuwa wata fuska ne) ".
(Musnad Ahmad, J:3, Sh:136).
Saboda haka idan an nema kuma kana da shi, to, ka bayar kawai ba tare da zargi/tunanin yadda za a sarrafa ta ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137925034/08126385470
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com