Hattara Musulman Kaduna, El-Rufai Rura Wutar Rikici Yake Yi!

 

Daga Ammar M. Rajab 


Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya ce ba zai bari wadanda ya kira da 'criminals' su sha ruwa ba a jihar. Kuma kudaden da gwamnatocin baya su ka rika ba su domin zaman lafiya ya wanzu a jihar, ba zai ci gaba da ba su ba. Kuma zai tabbata duk wadanda a cewarsa aka samu yana da hannu a rikicin Kudancin Kaduna a baya, za su kamo shi domin hukunta shi. 


Wadannan matakan da El-Rufai ke dauka, ya sanya wasu na ganin bajinta ne yake yi, kuma abin a jinjina masa ne, kuma a ganinsu, matakan da yake dauka, shi ne kawai zai kawo zaman lafiya a yankin da ake tashin hankalin. Ba komai ya sanya suke wannan tunanin ba, illa rashin hangen nesa. Domin kafin El-Rufai ya zama gwamna a Kaduna, an jima sosai ba a samu kazancewar rikici a yankin ba, me ya sanya yanzu rikicin ke 'kara ta'azzara a karkashin mulkinsa sabanin gwamnatocin baya?  


Idan El-Rufai ya manta, bari na tuna masa, shi ne da bakinsa a wata hira da ya yi cikin harshen Hausa da gidajen Rediyon Kaduna, ya ce; "yana biyan Fulani masu kashe-kashe a Kaduna" da sunan ramuwar gayya "domin su daina kashe al'umma". Harma yana cewa; "da a kashe rai daya a Kaduna, gwara baitul malin jihar Kaduna ya 'kare." 


Idan ya manta mun tuna masa. Idan abin mu tambaye shi ne, daga maganarsa zuwa yau, rai nawa aka kashe a Kaduna? Zai iya 'kirgawa? Ko Baitul Malin jihar Kadunan ya 'kare zuwa yanzu? Shiyasa ya kasa samun kudin da zai biya domin kare rayukan alummar da ake kashewa a kowacce rana? 


Su kuma masu murna da ana rikici a Kudancin jihar Kaduna, suna cewa matakan da El-Rufai ke dauka ya yi daidai, me ya toshe tunaninsu da ba sa hangen gaba? Ko suna tunanin Kadunar za ta ci gaba da kasancewa a aljihun El-Rufai ne?


Bari na shaida muku cewa; ku bar murna karenku ya kama zaki, duk ranar da reshe ya juye da mujiya a jihar Kaduna, fadowar ba zai yiwa kowa dad'i ba. Domin El-Rufai ba zai dawwama a mulkin jihar Kaduna ba, kuma 'karfin da yake tunanin zai sanya, ba zai ta6a kawo wa Kudancin Kaduna da ma jihar baki daya zaman lafiya ba. Idan sulhu ya kasa kawo zaman lafiya, 'karfi ba zai ta6a kawo wa ba. Yanzu duniya ta waye, 'karfi ba ya maganin rikici irin na kabilanci da nuna wariya. 


-AMR

17082020


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post