Ayi ka mutum ba qaramar daraja ba ce, domin kuwa idan aka yi ka dabba akwai wuyuwar barawo ya sace ka ya sayar, ko sarkin fawa ya sharara maka wuqa ko ayi ka qadangare kayi ta karakaina cikin ramukan kewayen mutane.
Sannan kuma ayi ka mutum musulmi babbar ni'ima ce wadda babu irin ta, domin kuwa idan da akwai sarki wanda zai kasance shine sarkin duk duniyar nan, to yin ka mutum musulmi shine yafi alkhairi da a yika mutum sarkin duniya ba musulmi ba.
Yin ka musulmi kuma ba za6in ka ba ne, ni'ima ce daga Allah, to yin ka musulmi yana nufin akwai abinda ya hau kanka na aiki wanda ya wajabta kayi domin nuna godiya ga ubangiji na yin ka mutum ba dabba ba, mutum musulmi ba mutum kafiri ba.
Haqqin da Allah ya aza maka a matsayin ka na musulmi shine biyayya da dukkanin umarnin Allah da ya saukar maka da kuma nesantar dukkanin abinda ya hana ka a littafin sa da ya aiko maka fiyayyen halitta shugaban Annabawa cikamakon Manzonni Annabi Muhammad (S) a matsayin mai gargadi agareka, agareki, agare ni, agare
ku, a gare mu baki daya mu da muka yarda da kadaitakar Allah da Manzoncin Annabi Muhammad (S).
Tambaya: Ta yaya zamu tsayu da wannan haqqin da Allah ya aza mana a matsayin mu na musulmi?
Amsa: Hanyar da za mu bi mu sauke wannan haqqin da Allah ta'ala ya aza mana shine watsar da dukkanin wasu dokoki Wanda ba Allah da ya halicce mu ne ya shata mana su ba, mu kawo littafin da mahaliccin mu ya aiko mana muyi aiki da dukkanin abinda ke ciki.
Wannan shine tsirar mu a duniya da kuma gobe qiyama. Wannan shine aikin da Allah ya aiko Annabawan sa sukayi, shine kuma abinda Maulana Sharafuddeen Sayyid Ibrahimul Zakzaky (H) ke kiran al'ummar qasar nan akai!!!
Kuma shine dalilin da yasa masu mulki su ka yi adawa da Annabawan Allah, kuma shine dalilin da ya sa mahukuntan Nigeria na dauri da na yau ke adawa da Sayyid Zakzaky suke yunqurin kashe shi.
Idan kace mana ai zagin sahabbai ya ke yi, sai mu ce maka to Annabi ibrahim, Musa, Isah, Nuhu da Annabin mu Muhammad wa suka zaga aka yi musu abinda aka yi masu?
KOMAWA GA DA'AWAR SAYYID ZAKZAKY (H) SHINE ZAI KAWO QARSHEN WULAQANCI, TOZARCI, YUNWA, TALAUCI DA MIYAGUN SHUGABANNI SUKA JEFA AL'UMMA DA YARDAR MUTANEN.
BA MALAM ZAKZAKY NE ZAI FITAR DA WANNAN QASAR YANAYI BA, ALLAH NE YAYI ALQAWARIN IDAN MUKA YI IMANI MU KA JI TSORON ALLAH, SAI ALLAH YAYI ALQAWARIN ZAI ZUBO MANA ARZIKI DAGA SAMA DA QASA acikin littafin sa WALAU ANNA AHLIL QURA AMANU WATTAQAU NA FATAHANA ALAIHIM BARAKATIN MINAS SAMA'I WAL ARDH, WALA KIN KAZZABU FA AKHAZNAHUM BI MA KANU YAKSIBUN
wannan alqawarin Allah ne, kuma ba ya sa6a alqawari.
Yan Nigeria ku dawo rakiyar mayaudara masu cewa zasu gyara muku qasa qarqashin tsarin yahudawa, ku dawo zuwa ga littafin ALLAH, Allah ba mutum ba ne ballantana kuyi tsammanin zai yaudare ku kamar yadda mai gaskiyar ku ya yaudare ku kuke yaudarar kawukan ku.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com