....!!!
...Umar Hassan Gololo...
Wannan Gwamnatin wacce take Jin kamshin jinin talakawan da suka zabeta, Gwamnatin da babu tausayin al'umma a constitution dinta, Gwamnatin da rayukan Sojojinta,'Yansandanta da talakawanta ba komai bane a wurinta idan dai zata farantawa Shugabannin Turai, Isra'ila da Larabawa.
Wadannan ma'adinan da Gwamna Matawalle na Zamfara ya niki gari takanas ta Gusau ya Kai wa shugaban Nigeria Buhari a fadar Aso Rock sune sanadin salwantar rayukan dubban daruruwan Mutanen Jihar Zamfara.
Kadan daga irin Wannan ma'adinan ne second scramble for Africa ya hana Mutanen kasar Mali zaman lafiya.
Duk Wanda Allahu Ta'ala ya Masa arzikin hankali ya San kashe-kashen da ake yi a Jihar Zamfara ya San tabbas akwai wani mummunan shiri a kasa.
Wai wadansu mahara ne akan babura kusan hamsin,dari daya,dari biyu, dari uku da dai sauransu suke zuwa kauyuka da safe,rana ko dare su kashe Mutane,su Kona rumbuna da gidaje,su kwashi Shanu da dukkan abinda suke bukata su tafi dasu cikin daji,amma har yanzu ba a San a Ina suke ba ballantana a San menene manufarsu.
Sun hana Mutanen yankin noma da kiwo, sun shafe kauyuka da yawan gaske,sun hana harkokin yau da kullum gudana a kauyuka da yawan gaske,amma Wai an kasa kawo karshensu duk da yawan Sojojin da 'yansandan da suke kashewa a kullum.
Mu dai Malam Zakzaky(H) ya fada Mana gaskiyar abinda yake faruwa a Arewa maso Gabashi da yammacin Nigeria da sunan Boko-Haram, Barayin Shanu da Kidnappers.
Ga Vedio jawabinnan ku kalla na Mlm Zakzaky (h)
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com