.
Bukhari ya taimaka sosai wajen cin zarafi Annabi ( S.A.W.W ), amma abin takaicin shine, da zarar ka ambaci irin wannan kalma ga Bukhari sai kaji WAHABIYAWA sunyi caah a kanka, domin su sunfi gamsuwa ace zarafin Annabi ( S.A.W.W ) kaci maimakon ka nuna kuskuren Bukhari.
.
Kar dai mu cika Ku da surutu, bari mu kawo irin gudumawar tasa kamar haka;
.
Muhammad Bn Bashari ya ba mu labari yace; Mu'azu 'Dan Hisham ya ba mu labari yace; Babana ya bani labari daga Qatadata yace; Anas Bn Malik ya ba mu labari yace;
" Annabi ( S.A.W.W ) ya kasance yana kewaye matansa ( da jima'i ) a lokaci daya (1) a dare da rana, a lokacin kuwa ( su matan ) suna su goma sha daya ne ( 11 ), yace; sai na cewa Anas; " Shin yana iya yin hakan ( yà sadu da matansa 11 cikin dare daya ) ?"
Sai yace; " To, mun kasance muna tattaunawa dai cewa shi an bashi qarfin ( jima'i ) na mutane talatin ne ".
.
Sai Sa'id yace; daga Anas, cewa mutane sun basu labari cewa ( adadinsu ) matan su tara ne "!
.
( Bukhari, Kitabul-Ghusli, Babi na 12, Hadisi me lamba 268 ).
.
======= DARASI =======
___________________________________
(i) - Annabi ( S.A.W.W ) ya kasance mai bayyana sirrin dake gudana tsakaninsa da matansa, Wanda duk wani mutumin kirki ba zai fito yana bayyana irin wannan sirri ga wasu ba, domin za a iya masa irin wannan kallo duk lokacin da aka ganshi.
.
(ii)- Sahabbansa sun kasance suna tattauna yanayin qarfin jima'insa a tsakaninsu.
.
(iii)- Kuma yana karantar damu cewa Annabi ( S.A.W.W ) ba shi da lokacin ganawa da Ubangijinsa saboda wannan haqqi na matansa da yake saukewa.
.
======= TAMBAYA =======
_____________________________________
.
(i)- Shin Annabin ne yake tara Ku yana sanar daku abinda ke wakana tsakaninsa da su na sirri?
.
(ii)- Idan hakane, to sai mu ce, ai cikin Hadisin babu inda aka nuna cewa shi ya fada muku da bakin sai.
.
(iii)- Idan kuma hakanne, Dan Allah meyi darasin hakan a gare ku?
.
(iv)- Idan kuwa ba shi ya fada muku ba, to ku kuke ke wata a kansa cikin dare adon ganin abinda yake yi?
.
(v)- Idan kuka tabbatar cewa shine ke fitowa yana muku irin wannan bayani, kuna nufin yana hana yin Abu ne shi kuma ya aikata?
.
(vi)- Yanzu dan Allah kunga yayi muku kyau ku zauna kuna tattauna irin wannan al'amari ga Ma'aiki ( S.A W.W )?
.
.
Bari dai mu leqa cikin wani Hadisi nasa muga abinda ya fada game da me bankada sirrin sa.
.
An riwaito daga Abu Huraira yace; Naji Manzon Allah ( S.A.W.W ) yana cewa;
.
" DUKKAN AL'UMMA TA ANA YI MUSU YAFIYA ( Afuwa ) SAI DAI MASU BANKADE ( revealing secret ). YANA DAGA CIKIN MASU BANKADE MUTUM YA AIKATA WANI AIKI ( na sirri ) DA DADDARE, SANNAN YA WAYI GARI ALLAH YA RUFA MASA ASIRI ( babu Wanda yasan abinda yayi ), SANNAN YANA CEWA; " WANE, JIYA FA NA AIKATA KAZA-DA-KAZA !" ALHALI FA YA WAYI GARI UBANGIJINSA NA RUFA MASA ASIRI, SHI KUWA YA WAYI GARI YANA YAYE SITIRAR DA ALLAH YAYI A KANSA ".
.
Muslim ne ya riwaito.
.
( Riyadus-Salihin, Babun rufawa musulmi asiri da hani game da yayatata in ba bisa lalura ba, Hadisi me lamba 240 ).
.
======= DARASI =======
_______________________________________
(1)- Allah yakan yàfewa mutum laifinsa ( in dai ba shirka bane ).
.
(2)- Duk masu bankade sirrin junansu ba a yi musu yafiya.
.
(3)- Allah na son rufawa kai asiri.
.
(4)- Kuma ba ya son me bankada sirrinsa.
.
======= TAMBAYA =======
_________________________________
(1)- Shin wannan Hadisin ya inganta?
.
(2)- Idan ya inganta, to kuna nufin shi Annabi ( S.A.W.W ) ba ya kwadayin wannan yafiyar ne?
.
(3)- Ashe ba shine ya samu shaida kan kyawawan dabi'u ba?
.
(3)- Idan kuwa shine, Ashe ba zan kira Hadisin farko a matsayin Hadisin cin zarafin Annabi ( S.A W.W ) ba?
.
(4)- To, Dan Allah me Zai hana nace Wanda ya kawo Hadisin ya nasa gudumawa wajen wannan cin zarafi tunda ya kira Hadisin nasa a matsayin ingantacce ?
.
FREE ZAKZAKY!
.
FREE ZAKZAKY!!
.
FREE ZAKZAKY!!!
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com