Free Zakzaky: Har Yanzu Ana Fita Abuja Struggling Daman?

 


Sau da yawa iyawa kana tattaunawa da wasu ƴan uwan na cikin harkan nan kuma mabiya saiyid zakzaky (h) sai kaji irin wannan tambayar ta fito daga bakin su!!!


Dayawa daga cikin ƴan uwa yanzu tunanin su yabar batun nemawa Sayyid zakzaky ƴanci yakoma program


Bawai kuma Inna suka dayin program bane, domin raya al'amarin iyalan gidan Manzon Allah ne wanda hakan gaba yake da komi a Duniyar nan!!!


To amman ɗan uwa karka Mance a Abuja ma anayin wannan program ɗin sannan ana fita nemawa jagora ƴanci duk da haka.


To meyasa muke kautar da tunanin mu akan lamarin jagoran mu? Idan mu ƴan uwa muna burus da lamarin jagoran mu to ina ga kuma sauran al'ummar musulmi dama waɗan nan azzalumai?


Fitar da ake ayi motsi a Abuja yana isar da saƙon da babu a inda zakai muzahara ko wani abu yakai nacan isar da saƙo!!!


Mun san Abuja itace zuciyar ƙasa, kuma matattarar azzalumai, wanda zuciyar su take ƙaɗawa da zarar sun ganmu mun fito.


Fitar mu a Abuja yana nunawa duniya cewar har yanzu ba'a saki jagoran ƴan shi'ar nan ba ashe?


Irin haka zakaji mutane suna magana' wanda daga nan sai kaji sun samu abin tattaunawa, wasu na tsinuwa wasu na addu'ar Allah yaƙwato shi!!!


Idan ka lura fitar muce take nuna musu lalle munanan kuma su Sayyid zakzaky har yanzu suna hannu.


Allah badan halin muba, badan raunin mu da sakacin muba, Allah ka ƙwato mana Sayyid zakzaky daga hannun waɗan nan miyagun azzaluman.


Abba Gano



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post