Fita Ma Biyu: Makircin DSS Ga Harka Islamiyya –Wani Abin Lura



A duk lokacin da jami'an tsaron kasarnan imma 'yan sanda, wa imma sojoji, NIA, DSS da ma kowanne bangare suka shirya wata kitumurmura, makirci da tuggu, sai ka ga wauta da shirme a cikinta tsagwaronta. 
Wani lokacin ba wai don ba su san abin da Harkar ta Musulunci ta doru a kai bane, a'a, sai don kawai tsabagen ayyukansu ya doru ne akan mugunta da 'kin hanyar Allah ta'ala tare da fada da adalci da kawwana zalunci. 
Harkar Musulunci a karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky, tafiya ce ta Musulunci wacce ta dora akan manufar "neman uzuri a wurin Allah," a yayin da ka tsinci kanka a al'ummar da ba sa bin dokokin mahaliccinsu a matsayin shari'arsu. 
Haka tafiyar ta faro tun cikin saba'inoni, yanzu fiye da shekara 40 ke nan. Jagoran tafiyar, Malam (H), ya ta6a bayyanawa a wani jawabinsa cewa; bai shelantar wannan da'awar domin wani ya bi shi ba, bilhasalima ma ya dauka, daga lokacin shi ke nan, za a shahadantar da shi ne. 
Tun daga wancan lokacin har zuwa yau, Shaikh Ibraheem Zakzaky bai ta6a sassautawa azzalumai ba, kullum cikin da'awar adalci yake da yiwa zalunci kule. Da kuma kira akan a komawa hanyar Musulunci, domin mafitar dukkanin matsalolinmu yana cikin Musuluncin nan. Sannan gaskiyarsa da amanarsa da fifita Musuluncin nan akan komai, da fawwalawa Allah dukkan lamuransa, ya sanya ya zamo mara sa'a kaf cikin masu da'awar Malinta a kasarnan. 
Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya zamo bawan Allahn da ya yi ilimi yake kuma aiki da ilimi. Kamar yadda kofar Ilimi, Imam Ali (A.S) ya lurantar da cewa; shi ilimi da aiki, tagwaye ne. Suna tafiya a tare ne. Idan har babu ilimi, babu aiki, idan babu aiki, babu ilimi. Wadannan suna daga cikin sirrin nasararsa da tasirinsa a zukatan al'umma. 
Gami da 'karawa, tunawa da Masa'ib na Abi Abdullahil Husain (A.S), ke kara masa juriya, dakewa da hakuri. Duk da dimbin jarabawowi da yake ci gaba da fuskanta. 
Da wannan nake sake tunatar da mahukumta kasarnan da masu sanya su aiki cewa: irin bawan Allahn da suke fada da shi ke nan a koyaushe, kuma idan har duniyarnan da muke ciki, da dukkan sauran halittu, Allah ta'ala ne ya halicce su, babu ranar da makircinsu zai yi tasiri akansa. Sai dai hakan ba yana nufin zamu zurawa makircinsu ido bane, mu ma zamu kalubalenceku ga dukkannin abin da muka iyawa.  
Bari na dawo kan makircinsu na kwana-kwanan nan wanda suke kitsawa Harkar Musulunci ta hanyar fakewa da cewa "Ammar Muhammad Rajab" na rabawa "matasa kudi" domin "tayar da yamutsi da hargitsi" a birnin tarayya Abuja da sauran sassan kasarnan, har suna aikawa shugabannin tsaron Jihohin kasarnan a matsayin "rahoton sirri." Wannan makirci ne kawai da gwamnatin Manjo Janaral (mai ritaya) ta shirya domin ci gaba da aiwatar da kwangilar da ta karbo a hannun Amurka da Isra'ila wanda Saudiyya ke biyan kudin. Kuma gwamnatin Manjo ta fara kaddamarwa tun a watan Disamban 2015. 
So suke kowa ya yi shiru, a manta da batun #ZariaMassacre, a kuma daina ambaton #FreeZakzaky da #JusticeForZakzaky. Idan ba haka ba, tun bayan ta'addancinsu kan Harkar Musulunci a 2015 da sauran ta'addancin da suka ci gaba da kaddamarwa akan Harkar har zuwa yau, mene ne wani abu da aka yi shi a 6oye? Kullum cikin cewa ake #FreeZakzaky. Ko da suka ce sun ayyana Harkar Musulunci a matsayin "'Yan ta'adda", mene ne aka aikata da ya wuce #FreeZakzaky? 
Shin Harkar Musulunci akwai wani boyayyen manufa da take da shi ne? Ita dai Harkar Musulunci manufofinta a bayyane suke kamar hasken rana da farin wata. A don haka duk wani makircin makirai, da kullin masu kulli, insha Allah ba zai yi nasara ba. 
-Ammar M. Rajab 06082020

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post