Duk Wata Daraja Ta Sahabi Umar da Za'a Kawo Sai Anci Mutuncin Annabi (S) !!!


Ni dai ban san dalilin hakan ba, duk wata daraja ta Umar da za a kawo sai anci mutuncin Annabi (S.A.W.W) sannan kaga ta fito.
*
Ga dai misali kamar haka.
*
Bukhari ya riwaito cewa; Ishaq ya bamu labari, Ya'aqub Bn Ibrahim ya bamu labari, babana ya bani labari daga Salihu, daga Ibn Shihab yace; Urwatu Bn Zubair ya bani labari cewa; A'isha matar Annabi (S.A.W.W) tace; Ya kasance Umar Bn Khaddab yana fadawa matan Manzon Allah (S.A.W.W) cewa ka tsare matanka.
Tace, amma sai yaqi bai aikata ba. Matan Annabi (S.A.W.W) sun kasance suna fita da daddare.
Sai Saudatu Bnt Zam'ata ta fita, ita kuwa ta kasance mata ce doguwa. Sai Umar Bn Khaddab ya ganta daga wajen zamansu sai yace; NA SANKI YA SAUDATU; Yana kwadayin a saukar da ayar Hijabi.
Tace; sai Allah ya saukar da ayar Hijabi ."
*
(Bukhari, H:6240)
*
== TAMBAYA ==
*
-Dan Allah yaushe Umar yasan darajar mace da zaiyi kwadayi ta sanya Hijabi?
*
-Kuma a wajen wa yasan cewa mace na da daraja?

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post