BAYANI A TAKAICE KAN RANAR GHADEER KHUM


Tare da Aliyu Samba

Ranar Ghadeer na daga muhimman ranaku da tarihi musulunci bazai taba cika ba Sai an ambace shi, rana ce da ta zo da wani muhimmin al'amari a duniyar musulunci, rana ce da akai abinda ba a taba yin irinsa ba, ba Kuma za a sake ba har kiyama ta tashi.

Ghadeer khum wani tafki ne dake garin makkah wanda a yau shine miqatin Yan afrika lokacin gudanar da aikin hajji. Sanannen abu ne cewa Annabi SAWA sau daya ya taba yin aikin hajji a rayuwar sa, shine hajjin da ake cewa Hajjatul Wadaa'i ma'ana hajjin ban kwana, Wanda yayi shi a shekara ta karshe a rayuwar sa. Bayan kammala aikin hajjin, Ma'aiki SAWA ya sa aka tara masa dukkan alhazai (sahabban da ke tare da shi a wannan lokacin) a wani wuri da ake cewa Ghadeer khum (wanda na ambata a baya), Allah SWT ya aiko da mala'ika Jibril da aya na cikin Suratul Ma'ida kamar haka;

“Ya kai wannan Manzo, isar da abin da aka saukar maka daga wajen Ubangijinka, in har bakai hakan nan ba kamar baka isar da sako bane.”

Bayan saukar wannan aya, manzon Allah SAWA ya gabatar da khudba a wannan wuri (Ghadeer khum) ga tarin sahabbai dake tare da shi wanda ruwayoyi suka nuna cewa sun doshi sahabi dubu Dari da ashirin da Hudu (absa sabani).

Manzon Allah SAWA yake cewa:

"Ni  'Mas'uli ne' (wanda Allah zai tambaya kan isar da sakon musulunci), Kuma ku ma mas'ulai ne (Ababen tambaya ne wajen Allah kan na Isar muku da sako). Sahabbai suka amsa da cewa:" hakika manzon Allah Sawa, Hakika ka Isar da sakon Allah garemu Kuma mun amsa"

A wannan lokacin ne Manzon Allah ya daga hannu sama yace:

"Ya Allah ka shaida sakon da na isar musu dashi sun shaida"

Sannan Manzon Allah SAWA yace zan bar muku abubuwa biyu masu daraja (Saqalaini) da in kun rike su Baza ku taba Bata ba a baya na, sune Alkur'ani da kuma Ahlulbait dina.

Sai Manzon Allah SAWA ya daga hannun Imam Aliyu (As) sama Yana mai cewa;

"Hakika Ubangiji Shine majibincin lamuran ku, ni Kuma nine shugaban dukkan halittu, to duk wanda na kasance shugaban sa, to Ali ma shugaban sa ne, Allah ka so wanda ya so Ali, kayi gaba da wanda yayi gaba da Ali, ka taimaki wanda ya taimaki Ali, ka tabar da wanda ya tabar da Ali"

Ruwayoyi sun tabbatar da cewa mutum na farko da ya fara tashi ya yiwa Imam Ali Mubaya'a shine Sayyadina Umar Bn Khaddabi, ya taso zuwa ga Imam Ali Yana fadin "Allah Kama, Allah kama, hakika ka wayi gari shugabana, shugaban dukkan wani mumini namiji ko mace"

A takaice wannan shine abinda ya faru a wannan Rana ta Ghadeer wadda a yau sashen muminai suke Raya ranar cikin ambato da yabon Imam Ali A.S.

Allah mun gode Maka da ka Sanya mu daga masu riko da wilayar Imam Ali A.S.

Eid Ghadeer Mubarak
©Aliyu Samba
07-08-2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post