Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi wannan Hudubar a wajen da ake kira Ghadir Kuma a ranar 18/12/10HJ. a Tsakiyar Dubban Sahabbansa.
Kashi na Uku. Ibrahim Daurawa.
...'Ya ku Mutane ku Fifita Ali akan kowa, saboda shi ne Mafi alkharin Mutane Mata da Maza a bayana Matsawar Allah yana sauko da arzikinsa kuma Halittunsa suna Wanzuwa.
'Yana cikin La'anta, yana cikin la'anta yana kuma cikin fushin Allah, yana cikin fushin Allah. Duk wanda ya yi watsi da wannan Jawabin nawa, ya kuma ki amincewa da shi.
'Saboda Hakika Jibril ya sanar da ni wannan daga Allah Ma daukaki. Wanda ya ce ' Duk wanda ya yi gaba da Ali, ya ki Sallamawa Jagorancinsa, la'anata da fushina ya tabbata akansa.
'Don haka Kowacce Rai ta lura da abin da aka saukar mata. Ta kiyaye (aiyukanku ga) Allah, don kada Kafafu su goce bayan tabbatuwarsu. Allah masanine ga duk abin da ku ke aikatawa.
'Ya ku Mutane Shi (Ali) ne Makusancin Allah (Janbullahi) kamar yadda aka baiyana a Littafin Allah. Allah Ta'ala ya ce 'Ya kaitona na yi watsi da aiyukana da makusancin Allah.'
'Ya ku Mutane ku yi dubi da tunani akan Ayoyin Kur'ani. Ku yi Nazari akan Ayoyin masu Ma'ana ta zahiri kada ku bi ma'anonin da suke a boye. Na rantse da Allah babu wanda zai iya Fassara muku Gargadi da al'ajabin da suke dauke shi, babu wanda zai iya Rarrabe tafsirinsu, face wanda nake rike da hannunsa na jawoshi a gareni( Sai ya daga Hannun Ali).
'Wanda nake sanar da ku cewa wanda duk nake Shugabansa ne, wannan Ali Shugabansa ne. Shi ne Ali Ibn Abu Talib, Dan Uwana, Wasiyina, wanda Nadinsa a Shugabanku an yi min Wahayinsa daga Allah mai girma da Daukaka ne.
'Ya ku Mutane hakika zan bar muku abubuwa nauyaya masu daraja guda biyu. Idan ku ka rikesu duka ba za ku bata ba har abada.
'Hakika Ali da Tsarkaka daga Tsatsona sune masu sassaukan nauyi , Kur'ani kuma mai nauyi sosai. Kowane daga cikinsu yana fassara dayan sun kuma nutsu da juna.
Ba za su taba rabuwa da juna ba har abada sai sun dawo gare a tabkin Kausara.(Ranar Kiyama).
'Ku shaida, su Ahlul Baity sune Amanar Allah a cikin Halittarsa da Mutane masu hikima a doron Kasa.'
Daga nan Manzon Allah (Saaw) ya kama Hannun Imam ya daga Sama ya ce.
' Ya kuma Mutane wanene yake da hakki akan ku fiye da rayukanku'
Suka ce ' Allah da Manzonsa ne"
Sai Manzon Allah (Saaw) ya ce ' Ku Shaida Wanda duk nake Shugaba a gareshi, wannan Ali Shugabansa ne. Ya Allah ka dafawa wadanda suka tsaya kyam wajen biyayya a gareshi, Ka yi adawa wadanda suka yi adawa da shi, Ka taimaki wadanda suka taimakeshi. Ka tabar da wadanda suka tabar da shi.'
'Ya ku Mutane wannan Ali dan Uwana ne, Wasiyina ne, Magajin Ilimina ne, Khalifan al'ummata a bayana da Tafsirin Littafin Allah Mai girma da Daukaka. Mai Kira ne na Hakika zuwa ga Gaskiya.
' Shi ne wanda yake aikata abin da Allah yake So, Yake yakar Makiyansa, ya ke umarni ga yi masa da'a, ya ke hani ga sabawa umarnin Allah.
'Tabbas shi Khalifan Manzon Allah ne, kuma Amirulmumina, Imami mai Shiryarwa. Mai Halaka masu Warware Bai'a da Yan ta'adda da masu yin Ridda.
'Ina magana da umarnin Allah, maganata baza ta sauya ba.
'Ina fada da Umarnin Allah. Ya Allah ka zama Waliyi ga wanda ya riko da shi.
'Ka yi gaba da wanda ya yi gaba da shi'
'Ka la'anci wanda ya yi watsi da shi'
'Ka yi fushi da wanda ya danne masa hakkinsa'
'Hakika yanzu na kammala aikina, Hakika yanzu na isar da sakon, hakika na sanar da ku, Hakika yanzu na faiyace shi'
'Tabbas Allah Mai Girma da daukaka ya fada haka kuma na sanar a madadinsa.
'Hakika babu wani Amurulmumina face wannan dan uwan nawa. Kuma bai Halatta ba a kirawo wani bayan shi da Sunan 'AmirulMumina' bayan na yi Wafati.
Daga Littafin 'The Sermon of Prophet Muhammad (Saaw) at Ghadir Kum'
Zan shi ci gaba gaba Insha Allah.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Tunatarwa