" Babu wanda ya rage daga cikin wadanda suka yaqi Hussaini face anyi musu Uquba a duniya kafin lahira.


ADA SUKA AUKU SAKAMAKON KISAN IMAM HUSSAINI (A S) !!!

Ma'asumah Nigeria news Update

Duk gurbacewar abubuwa da jujjuya tarihi, sahihin tarihi ba zai taba bacewa ba, domin an kawo shi cikin littattafai masu yawa daga Sahabban/
malamai daban-dabam.
Abu na farko da ya faru kuma ya zama wajibi ga dukkan mumini yayi koyi da shi shine kukun halittun Allah (T).
(1)- Ada'i Bn Yasari ya kawo cewa, yayin da aka kashe Imam Hussaini (A.S) Sama tayi kuka, kukun nata kuwa shine Jan (red) da tayi.
Ibn Abiy Hateem shima ya kawo qarqashin Tafsirin aya ta 29 cikin Suratul-Dukkhan,
" FAMAH BAKAT ALAIHIMUS-SAMAA'A WAL ARDHI "
yake cewa; " Babu wani Dutse da za ka duba face jini na kwarara a qarqashinsa, kuma Rana tayi Khusufi, sannan sararin samaniya yayi ja na tsahon watanni hudu (4)."
(Ibn Kasir, J:4, Sh:154-155).
Zuhriy kuma cewa yayi, " Ya iso min cewa, babu Dutsen da za ka leqa daga cikin Dutsin Baitul-Maqdis ranar kisan Imam Hussaini face kaga jini na gudana qarqashinsa, kuma duniya tayi duhu sau uku (3) a ranar da aka kashe Hussaini ."
(Nurul-Absar, Sh:214).
(2)- Halakar maqiya.
Zuhriy ya sake kawowa cewa;

" Babu wanda ya rage daga cikin wadanda suka yaqi Hussaini face anyi musu Uquba a duniya kafin lahira. Ko dai ta hanyar kisa, ko baqanta fuska, ko jirkita halitta, ko kuma gushewar mulki a qanqanin lokaci ."

Sabadi Ibn Jauziy ya riwaito cewa;
" Wani tsoho ya halarci yaqarsa kadai, sai ya makance. Da aka tambaye shi dalilin haka sai yace; Na ga Annabin Allah (S) be shimfide akan Zira'insa, kuma a hannunsa akwai Takobi (swarm), kuma a hannunsa akwai wani mazubi cikinsa akwai mutane goma (10) daga wadanda suka kashe Hussain a yanyanke. Sa'annan ya tsine min ya zage ni, sannan ya watso min wani saura daga jinin Hussaini, shine na wayi gari a makance ."

Sannan an sake riwaitowa cewa, wani mutum ya lanqaya (hanging) kan Imam Hussaini (A.S) a wajen daure Dokinsa, bayan wasu kwanaki sai yayi mafarki, sai fuskarsa tayi baqi-qirin fiye da baqin baqin Biri."

Zamuci Gaba insha Allah...
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com




Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post