Ni idan za'a tambaye ni menene ake nufi da hamza lawal, zan fada muku cewa Hamza lawal yana nufin shirme, shirme kuma yana nufin hamza lawal, ma'ana idan a nutse zaka karanci surunbatuwar hamza lawal zaka kasa fuskantar komi illah dai ka samu zuwa ga natijar cewa asalin ma'anar Hamza lawal ana nufin shirme, shirbici, sokonci irin na wadanda linzamin rayuwa ya subuce musu tun lokacin suna almajirci a Hauza.
Zanso ace 'yan uwa su daina kula sunkuturun sabotagi hamza lawal domin babban ribar da hamza ke samu a kadafkarar sa bata wuce tamka masa da akeyi.
Idan usulubin silsilar hamza lawal za'a dauka a hukumta kowacce irin tafiya da ita tom ba addinin musulunci ba shi'anci ma za'a rushe shi ne gabadaya.
Wani abin lura, idan mashirmaci yana shirme ba'a tamka masa domin zarar ka tamka masa kun zam sammakal.
Kira na musamman da zanyi ga 'yan uwan mu na Ashabul kahfi, domin isar mutuncin Sayyida Fateema (S.A) kada ku saurari shirbicin wani wagili da akace ya zagi mai girma sarkin gida Amirul wa'izina, Maulana sheikh Dr. Abdujjabar Muhammadu Naseer Kabara.
Wallahi mu mun san shi sarai kuma domin ku sani ba wanda za'a tsaya ana bata lokacin tankiya dashi bane.
Ga 'yan uwa dama dai kun san wanene Hamza badikko saboda haka mu lura da abinda ke gaban mu, mu kyale wawa da wawaye su cigaba da cinikin su na wauta.
Yanzu kalubalen mu shine kokari domin kubuto da rayuwar Jagora (H)
Bissalam.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Daga marubata