Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya dora alhakin harin da aka kaiwa tawagarsa ranar Laraba ta makon jiya a kan sojojin Najeriya.
A ranar Larabar makon jiya ne aka kaiwa tawagar gwamna Zulum hari yayin da ya je kan hanyarsa ta zuwa garin Baga da ke karkashin karamar hukumar Kukawa a jihar Borno. Jaridar Premium Times ta rawaito cewa Zulum ya tsallake rijiya da baya yayin da aka kaiwa tawagarsa hari yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Baga domin rabon tallafi ga mazauna sansanin gudun hijira (IDP).
Da ya ke magana da kwamandan rundunar soji jim kadan bayan kaiwa tawagarsa harin, Gwamna Zulum ya nuna bacin ransa a kan yadda sojoji su ka gaza kwace garin Baga duk fa yawan rundunoninsu da ke jibge a yankin. "Kun fi shekara guda a nan wurin, akwai sojoji 1,181 a wannan yankin, idan ba za ku iya kwace garin Baga mai nisan kilomita 5 daga sansaninku ba, sai mu hakura mu manta da Baga.
"Zan sanar da babban hafsan rundunar soji idan ya so sai ya sauyawa sojojin da ke nan wurin da za a amfanesu," kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya rawaito Zulum na fadawa kwamandan sojojin. Da ya ke magana kwana daya bayan kai ma sa harin, Zulum ya ce abinda ya faru a kansa ba wani abu ba ne face kitimurmurar sojoji.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne yayin da wasu gwamnonin jam'iyyar APC a karkashin jagorancin shugabansu, Atiku Bagudu gwamnan jihar Kebbi, su ka kai ma sa ziyarar jaje a fadar gwamnatin jihar Borno da ke Maiduguri.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Labaran Duniya